You are here: HomeAfricaBBC2021 05 24Article 1269145

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Dutsen Nyiragongo: DR Congo na shirin kwashe mutanen wabi birni saboda amon wuta

Saboda awon wuta, babu wutar lantarki a yawancin sassan birnin Goma a Noth Kivu Saboda awon wuta, babu wutar lantarki a yawancin sassan birnin Goma a Noth Kivu

Gwamnatin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kong ta fara shirin kwashe dukkan mazauna birnin Goma da ke gabashin ƙasar bayan da wani dutse ya fara amon wuta.

Gagarumin narkakken dutse da wuta ke feso wa daga saman dutsen yana kuma kwarara, inda hayaƙi mai launin tsanwa ya turnuƙe birnin mai fiye da mutum miliyan biyu.

Ana iya ganin mutanen da su ka razana na ficewa daga birnin.

Wannan Dutsen mai nisan kilomita 10 daga birnin ya taba yin amon wuta a 2002 inda ya kashe mutum 250 baya ga raba mutum 12,000 da muhallansu.

Tun ma gabanin sanarwar da gwamnati ta fitar, ana iya ganin tarin mutane dauke da katifunsu da wasu kayayyaki, yawancinsu kafa, su na tserewa daga birnin inda su ka nufi kan iyakar kasar da Rwanda a gabas. Wasu kuma sun yi yamma da birnin inda akwai tuddai masu dama.

Wata mata da ke zaune a birnin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Akwai warin sinadarin sulphur mai karfin gaske. Daga nesa ana iya hango harshen wuta mai girma na fitowa daga saman dutsen".

An dai ba mutanen birnin shawara da su kwantar da hankulansu, amma wasunsu sun koka da yadda ba su samun cikakken bayanai kan abin da ke wakana, musamman ma yadda ake bayar da bayanai ma su karo da juna a shafukan sada zumunta.

Dario Tedesco masani ne kan duwatsu masu amon wuta da ke zaune a birnin na Goma, ya shaida wa Reuters cewa wani sabon tsagi ya bayyana a jikin dutsen, kuma narkakken dutse na isa filin jirgin saman birnin.

A halin da ake ciki, babu wutar lantarki a yawancin sassan birnin.