You are here: HomeAfricaBBC2023 02 09Article 1711397

BBC Hausa of Thursday, 9 February 2023

Source: BBC

Dubban mutane na son a ba su jaririya Aya, wadda aka haifa a karkashin ɓaraguzai

Jaririya da aka zakulo daga karkashin ɓaraguzan wani ginin da ya rushe a Syria Jaririya da aka zakulo daga karkashin ɓaraguzan wani ginin da ya rushe a Syria

Hoton wata jaririya da aka zakulo daga karkashin ɓaraguzan wani ginin da ya rushe a sanadin girgizar ƙasa a yankin arewa maso yammacin Syria ya ja hankulan jama'a masu yawa.

Yarinya wadda aka lakaba wa suna Aya da Larabci, an same ta ba a ma yanke cibiyarta daga jikin mahaifiyarta ba.

Sai dai ba mahaifiyarta kawai ta rasa ba, domin ta rasa mahaifinta da dukkan 'yan uwanta su hudu a sanadin inftila'in girgizar kasar da ta afkwa wa yankin.

Wani dan uwanta na nesa na wurin yayin da aka zaulo Aya daga ginin kuma ya kai ta wajen wani likitan kananan yara a birnin Afrin.

A halin yanzu tana samun kulawa a asibiti - sai dai wani abin al'ajabi na faruwa, inda dubban mutane a shafukan sada zumunta ke bayyana sha'awar a ba su Aya domin su kula da ita na tsawon rayuwarta.

Shugaban asiitin Khalid Attiah ya ce gomman mutane sun kira shi daga sassan duniya, suna bukatar a ba su damar renon ta.

Sai dai Likita Attiah - wanda ke da 'ya jaririya mai wata hudu da haihuwa ya ce: "Ba zan bari wani ya raba ni da ita ba a yanzu. Har lokacin da 'yan uwanta na nesa suka dawo, zan kula da ita kamar 'yata ta cikina."

A halin yanzu, matarsa ce ke shayar da Aya tare da tasu jaririyar.