You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848674

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Dortmund ba ta bukatar Sancho, Liverpool na zawarcin Rodrygo

Jadon Sancho Jadon Sancho

Borussia Dortmund ba ta da ra'ayin sake dawo da ɗan wasan Manchester United da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 23. (Bild - in German)

Yanayinda United ta soma da shi a wannan kaka ta Firimiya, ya yi kokarin gamsar da masu shirin sayanta, wato Sir Jim Ratcliffe ko Sheikh Jassim. (Daily Mail)

Liverpool ta shiga zawarcin ɗan wasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 22, idan ɗan wasan Masar Mohamed Salah mai shekara 31, ya bar ƙungiyar a cikin watan Janairu.(Fichajes - in Spanish)

Babu batun ɗan wasan tsakiya a Fulham da Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, na da damar barin ƙungiyar kafin cikar wa'adin kwatiraginsa a sabon yarjejeniyar da ya rattaɓawa hannu.(Football Insider)

Akwai wasu ka idoji a yarjejeniyar iya dawo da Harry Kane muddin Tottenham ta bukaci hakan daga Bayern Munich nan gaba. (Daily Mail)

Akwai batun bai wa Kane zaɓi duba idan ya shirya sake zama a ƙungiyar da Daniel Levy ke shugabanta. (Telegraph)

Tottenham na shirin gabatar da miƙa tayi ga ɗan wasan gaba a Koriya ta Kudu, Son Heung-min mai shekara 31, na sabunta zamanta a kungiyar da ke arewacin Landan har zuwa shekara ta 2025.(90min)

Chelsea ta ce a shirya take ta karɓi fam miliyan 400 daga wata kamfanin Amurka, da ke shirin zuba hannun jari a ayyukan sabon fillin wasanta da wasu shirye-shiryesu. (Telegraph)

Wannan zuba jari zai taimakawa Chelsea kasance ɗaya daga cikin kungiyoyi mafi girma tattalin arziki da kuma rage mata basuka a Stamford Bridge. (Goal)

Manchester City na shirin miƙa tayinta kan ɗan wasan Boca Juniors da Argentina Valentin Barco, mai shekara 19, a kan kuɗi fam miliyan 15 a watan Janairu. (Football Insider)

City na kuma son mallakar ɗan wasan Ingila mai buga ajin 'yan shekara kasa da 17, Divine Mukasa, mai shekara 16 daga West Ham. (Fabrizio Romano)

Manchester City ta yi watsi da tayin da aka gabatar mata kan ɗan wasanta mai buga gaba Oscar Bobb daga Ajax da Porto. (Telegraph)

Ɗan wasan Paris St-Germain Hugo Ekitike, mai shekara 21 na shirin gwabza gumurzu kan makomarsa a ƙungiyar ta Faransa, duk da cewa yana sane da tayin da ake kawo wa a kansa daga kungiyoyin firimiya irinsu Crystal Palace da Brentford da Everton da West Ham United da kuma Wolves. (90min)

Huddersfield Town ta shirya naɗa tsohon dan wasan Sheffield Darren Moore, mai shekara 49, a matsayin sabon koci domin maye gurbin Neil Warnock da ta raba gari da shi. (Sun)

Tsohon ɗan wasan Italiya Vincenzo Montella, mai shekara 49, na shirin zama kocin tawagar 'yan wasan Turkiyya. (Fabrizio Romano)

Manchester United na shirin bai wa ɗan wasanta na gaba mai shekara 19 Joe Hugill sabon kwantiragi. (Manchester Evening News)