You are here: HomeAfricaBBC2023 02 13Article 1713533

BBC Hausa of Monday, 13 February 2023

Source: BBC

De Gea ya yi wasan Premier na 400 a Man United

David de Gea David de Gea

Ranar Lahadi Manchester United ta ci Leeds United 2-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier League a Elland Road.

United ta fara cin kwallo ta hannun Marcus Rashford, sannan Alejandro Garnacho ya kara na biyu.

David de Gea ne ya tsare ragar United, kuma wasa na 400 da ya yi kenan a Premier League.

Ya zama na farko da ba dan Birtaniya ba da ya yi wasa da yawa a babbar gasar tamaula ta Ingila a ttarihi.

Golan ya tsare raga sau 139 da kwallo bai shiga ragarsa ba, an kuma yi nasara 216 da shi a United da shan kashi a fafatawa 87.

Cikin wasa 400 da ya yi, kwallo 431 ne ya shiga ragarsa a Premier League da yin kuskuren da aka ci United karo 16, ya kuma ci gida sau daya.

Tsohon golan tawagar Sifaniya ya hana kwallo 119 ya shiga ragarsa wato Saves a babbar gasar tamaula ta Ingila da tare fenariri hudu.

De Gea ya lashe Premier League a 2012/13 ya karbi kyautar dan wasan da yafi taka rawar gani a watan Janairun 2022.

Shine ya lashe kyautar safar hannu ta zinare a matakin ba kamarsa a yin bajinta a kakar 2017/18.

De Gea mai shekara 32 ya karbi katin gargadi shida a wasannin Premier League, wanda ba a taba yi wa jan kati ba a gasar.

Ya koma Old Trafford kan fam miliyan 19 daga Atletico Madrid a shekarar 2011, tun daga lokacin ya zama na daya a tsare ragar United kawo yanzu.