You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817384

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Darasi huɗu daga tuhumar maguɗin zaɓe da ake yi wa Trump

Donald Trump Donald Trump

Masu bincike na musamman kan yunƙurin tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na jirkita sakamakon zaɓen 2020 sun tuhume shi kan laifuka guda uku.

Tuhumar mai shafi 45 ta zargi Trump da shirya maƙarƙashiyar da za ta ba shi damar ci gaba da mulki duk da kayen da ya sha a hannun Shugaba Joe Biden.

Haka kuma, ta zarge shi da yaɗa "ƙarairayin raba kan jama'a" da gangan game da maguɗin zaɓe, abin da ya yi wa Amurka da dimokraɗiyyarta barazana.

Mista Trump ya siffanta tuhume-tuhumen - karo na uku ke nan da yake fuskanta - a matsayin "bi-ta-da-ƙullin da ya saɓa da al'adar Amurka" a kansa.

Tuhumen-tuhumen sun ƙunshi haɗa baki wajen zambatar Amurka da haɗa baki wajen kawo cikas ga tsarin doka da kawo tsaiko ga tsarin doka da kuma haɗa baki wajen daƙile 'yanci.

Wasu ƙwararru a ɓangaren shari'a na cewa abu ne mawuyaci a iya fito da hujjar cewa Trump ya aikata laifuka, kuma akwai yiwuwar a bayyana abubuwan da ya aikata da waɗanda ya faɗa a matsayin waɗanda suka dace da tanadin kundin mulkin Amurka da aka yi wa kwaskwarima.

Ga darasi huɗu da muka koya daga tuhumar da Ma'aikatar Shari'a ke yi wa Trump.

1. Ana zargin Trump da haɗa-baki kan abubuwa masu yawa

A cikin tuhumar, mai shigar da ƙara na musamman Jack Smith bai fayyace abu ɗaya takamaimai ba, kamar farmakin ranar 6 ga watan Janairun 2021 a kan Majalisar Amurka.

A madadin haka, sai ya mayar da hankali a kan dukkan abin da ake zargin sa da aikatawa a tsawon wata biyu, tun daga washe garin ranar zaɓe zuwa ranar da ya bar ofis.

"Duk da shan kaye, wanda ake tuhuma [Trump] ya zaɓi ya ci gaba da zama a kan mulki," a cewar takardar tuhumar a shafin farko.

"Saboda haka, fiye da wata biyu tun daga washe garin ranar zaɓen 3 ga watan Nuwamba, Trump ya dinga yaɗa ƙarairayi cewa wani abu zai iya faruwa da sakamakon matuƙar bai yi wa wasu daɗi ba, kuma shi ne ya yi nasara."

Masu shigar da ƙarar sun kuma bayyana abu uku da suke ganin sun saɓa wa Sashe na 18 na Dokar Amurka:

Haɗa baki kan yunƙurin zambatar Amurka ta hanyar yaudara, da kawo cikas kan yadda gwamnati ke tattarawa da ƙirgawa da kuma amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Haɗa baki wajen yunƙurin ɓata darajar takardun shaidar amincewa da sakamakon zaɓen da Majalisa ta yi a ranar 6 ga watan Janairu.

Haɗa baki don hana wa wasu 'yancinsu na kaɗa ƙuri'a da kuma hana a ƙirga ƙuri'un nasu.

2. Zargin Trump da haɗa baki da wasu mutum shida

Masu tuhuma sun ambaci wasu mutum shida da ake zargin Trump ya haɗ baki da su ta haramtacciyar hanya don sauya sakamakon zaɓen ta hanyar matsa wa masu ƙirga ƙuri'a su shashantar da batun ɗaiɗaikun ƙuri'u da kuma maye gurbin ingantattun ƙuri'u da na boge.

Kundin tuhumar bai ambaci sunayensu ba, amma ana iya gane biyar daga cikinsu saboda yadda aka siffanta ayyukansu sun yi kama da waɗanda mutane suka riga suka sani.

Na 1 an bayyana shi da lauya mai yaɗa iƙirari da gangan kan yaƙin neman zaɓen Trump, wanda ya yi kama da Rudy Guiliani, a cewar lauyan Trump cikin wata sanarwa.

Bayanan da aka bayar kan mutum na 2 sun yi kama da John Eastman.

Mutum na 3 da na 4 da na 5, kafofin yaɗa labarai sun ce tsohon lauyan Trump ne Sidney Powell, da Jeffrey Clark, da Kenneth Chesebro, amma babu wanda ya ce komai daga cikinsu zuwa yanzu.

Ba a iya gane ko wane ne mutum na 6 ba.

3. Trump ya ci gaba da yaɗa ƙarairayi kan maguɗin zaɓe da gangan

Tuhumar ba ta zargi Trump da yaɗa ƙarya ba kawai - ta ce yana sane da cewa abin da yake yaɗawa game da sakamakon zaɓen ba gaskiya ba ne.

"Wanda ake tuhuma ya maimaita kuma ya ci gaba da yaɗa su duk da haka - don ya nuna ƙarairayin nasa na gaskiya ne, da haifar da ruɗani a ƙasa da kuma cusawa mutane ƙiyayyar tsarin gudanar da zaɓe."

Masu shigar da ƙara na gwamnati na cewa wannan na cikin manyan salonsa na ci gaba da zama a kan mulki.

4. Trump ka iya kare kansa game da 'yancin faɗar ra'ayi

Jack Smith ya aminta cewa Mista Trump, kamar kowane Ba'amurke, na da 'yancin ƙalubalantar sakamakon, kuma zai iya yin iƙirarin cewa an kayar da shi ne saboda maguɗin zaɓe.

Wannan ɓangaren na 'yancin faɗar ra'ayi da ke cikin Gyaran Kudin Mulki na Farko, ita ce babbar matsalar da masu shigar da ƙara ya zama wajibi su shawo kanta.

Ƙwararren lauya mai ra'ayin riƙau, Jonathan Turley, wanda ya goyi bayan tuhumar da aka yi wa Trump kan ɓoye takardun sirri, ya faɗa a Twitter cewa "Jack Smith ya gabatar da tuhuma ta farko kan zargin yaɗa labaran ƙarya".

"Wasu daga abubuwan na da kariya daga kundin mulki, a cewar Mista Huq na Sashen Shari'ar Jami'ar Chicago. Amma ya ce: "Kalaman da aka yi wajen aikata laifin ba su da kariya a kundin mulkin."