You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848653

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Daniel Levy na iya sayar da hannun jari a Tottenham

Yan adawa na neman Levy ya marabus Yan adawa na neman Levy ya marabus

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, Daniel Levy ya ce zai iya sayar da hannun jarinsa a kungiyar idan yin hakan yana da fa'ida ga kulob din.

Levy ne ke tafiyar da harkokin kulob din a madadin kamfanin ENIC wanda ya mallaki kashi 86.5%, yana kuma rike da mukamin shugaba tun 2001.

Magoya bayan kungiyar kwallon kafar sun yi kira ga Levy da ya ajiye mukaminsa sakamakon rashin kokarin da aka yi a kakar wasan da ta gabata.

Hankali ya dan kwanta a Tottenham a kakar wasar bana bayan nadin Ange Postecoglou a bazara, amma batutuwan da ke tasowa a wajen filin wasa sun sa an ci gaba da hura wa Levy wuta.

Dan kasuwan mai shekaru 61, ya tabbatar da cewa a baya bangarori da dama sun nuna sha’awarsu na mallakar kungiyar, musamman tun bayan da suka koma sabon filin wasa mai daukar yawan mutane 62,850 a shekarar 2019.

Ya bayyana cewa idan wani ya gabatar da tayi mai mahimmanci ga Tottenham, za a iya tattaunawa.

Kuma idan aka ga yana da muradin kulob din komai na iya faruwa.