You are here: HomeAfricaBBC2023 12 17Article 1900184

BBC Hausa of Sunday, 17 December 2023

Source: BBC

Dan shekara 17 ya zama matashin da ya ci kwallo a Premier a tarihi

PL logo PL logo

Dan shekara 17 na Newcastle United, Lewis Miley ya zama matashin da ya ci kwallo a tarihi a Premier League.

Ranar Asabar Newcastle ta doke Fulham da ci 3-0 a St James Park a wasan mako na 17 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Fulham ta buga wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Raul Jimenez jan kati a minti na 22, bayan wani tsalle da ya yi, ya doki fuskantar, Sean Longstaff.

Tun farko alkalin wasa Sam Barrott ya bai wa Jimenez katin gargadi mai ruwan dorawa daga baya mai kula da VAR, Michael Salisbury ya sanar da Barrott ya je ya kara kallon abinda ya faru.

Bayan da raflin ya kammala kallon abinda ya faru a VAR, sai ya soke katin gargadi ya kuma zaro jan kati ya daga masa.

Anthony Gordon ya buga kwallo ya bugi turke tun kan hutu, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Lewis Miley ya ci kwallon.

Mai shekara 17 da kwana 229 ya zama matashin da ya zura kwallo a raga a Premier League, tun bayan Federico Macheda na Manchester United a Afirilun 2009, mai shekara 17 da kwana 226 a lokacin.

Miguel Almiron ne ya kara na biyu daga baya Dan Burn ya ci na uku da Newcastle ta hada maki ukun da take bukata.

Wannan sakamakon ya kawo karshen wasa uku a jere da aka ci Newcastle, kwana uku tsakani da AC Milan ta ci 2-1 a St James Park a Champions League.

An fitar da Newcastle daga gasar zakarun Turai, wadda rabonta da wasannin tun bayan shekara 20.