You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896713

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Dan kallo ya mutu ana tsaka da wasan Granada da Bilbao a La Liga

Hoton alama Hoton alama

An dage wasan Granada da Athletic Bilbao a gasar La Liga ranar Lahadi, bayan da wani dan kallo ya mutu a sitadiya da ake kira Nuevo Los Carmenes.

Ana tsaka da wasa a minti na 18 a lokacin Athletic ta ci kwallo ta hannun Inaki Williams, sai aka dakatar da wasan.

'Yan kwallon sun fice daga filin a minti na 20 daga baya aka bukaci magoya baya da kowa ya kama gabansa.

Mahukuntan La Liga sun sanar da dage karawar ta kuma ce za ta sanar da ranar da za a sake fafatawar ta mako na 16.

Granada ta fitar da jawabi cewar ''An dage wasan nan take sakamakon da wani mai goyon bayanta ya mutu - tana kuma mika ta'aziyya da iyalansa.''

Magoya bayan Granada sun yi ta yi wa golan Athletic, Unai Simon tafi, bayan da ya je ya sanar da jami'ai mutuwar dan kallon.