You are here: HomeAfricaBBC2022 12 30Article 1687985

BBC Hausa of Friday, 30 December 2022

Source: BBC

Daga Pele muka koyi ƙwallon da har ta sa muka shahara – Tijjani Babangida

Yan wasan Brazil da hoton Pele Yan wasan Brazil da hoton Pele

Al'ummar duniya na ci gaba da jimamin mutuwar fitaccen ɗan ƙwallon duniyar nan, Pele wanda ya mutu yana da shekara 82.

Ana ganin Pele wanda ya mutu ranar Alhamis, a matsayin ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irinsa ba a duniya, kuma sau uku yana taimaka wa Brazil wajen lashe Gasar cin Kofin Duniya.

Tijjani Babangida, ɗaya daga cikin tsoffin gwarazan 'yan ƙwallon Afirka kuma tsohon ɗan wasan Super Eagles ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa mutuwar Pele babban rashi ne ga duniyar ƙwallon ƙafa, ba kaɗai ga Brazil ba.

A cewarsa, "mutuwar Pele ta taɓa duk wani mai sha'awar ƙwallo da wanda ke sha'awar abubuwan da Pele ya yi" a lokacin da yake raye.

Ya ce Pele ya zama abin koyi a gare shi da sauran ƴan ƙwallo da suka taso tare kasancewar "tun muna yara bidiyon Pele muke kallo da kuma ƙwallayen da Pele ya ci, duk su muke kalla, har ya kasance mu ma mun zama ƴan ƙwallo." in ji Tijjani Babangida.

Tsohon ɗan wasan Najeriyar ya ƙara da cewa zai yi wuya a manta da Pele saboda gudunmawar da ya bayar a fagen ƙwallon duniya.

Haɗuwata da Pele babban tarihi ne a gare ni...

Tijjani Babangida ya bayyana cewa ya sha mamaki lokacin da haɗu da Pele karon farko a rayuwarsa har suka yi musabiha.

A cewarsa ya fara haɗuwa da shi ne a lokacin da yake taka leda a ƙungiyar Ajax inda aka gayyaci Pele a matsayin baƙo na musamman a farkon kakar wasa.

"Abin mamaki gare ni lokacin da na ganshi ya shigo cikin fili, ya dumfaro ni, ya miƙo min hannu muka gaisa, na riƙe shi na faɗa masa ina matuƙar (goyon bayansa), kai ne (gwarzona), na fara ƙwallo saboda shi, ina ta kallo yana ta dariya."

Tijjani Babangida ya ce duk da cewa sau ɗaya ya taɓa haɗuwa da marigayin, amma "ko lokacin da na gan shi, mutum ne kullum, ko a bidiyo ka gan shi, mutum ne mai son dariya."

Ya kuma bayyana yadda a lokacin da suke harkar ƙwallo suke kwaikwayon salon buga ƙwallon Pele da yadda yake nuna murna idan ya ci ƙwallo da kuma yadda ya ƙware wajen iya yanka.

Duniyar ƙwallo ta kaɗu...

Su ma fitattun ƴan ƙwallo a duniya da sauran masu ruwa da tsaki a fagen wasanni na ci gaba da miƙa saƙon ta'aziyya kan mutuwar shahararren ɗan wasan Pele.

Shugaban hukumar Fifa Gianni Infantino ya bayyana cewa "wannan rana ce da bamu so ta zo ba - ranar da muka rasa Pele."

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Infantino ya bayyana irin nasarorin da Pele ya samu a lokacin da yake tashe.

Ya kuma bayyana Pele a matsayin abin koyi da kuma yadda yake mutunta sauran abokan karawarsa."

Shi kuwa ɗan wasan Brazil Neymar, a shafinsa na Instagram, ya bayyana mutuwar marigayin a matsayin gagarumin rashi ganin yadda ya fito da ƙasarsa a fagen ƙwallon ƙafa.

"Zan iya cewa kafin Pele, ƙwallon ƙafa wasa ne kawai. "Pele ya canja komai. “Ya sauya ƙwallon ƙafa zuwa wani abin nishaɗi." in ji Neymar.