You are here: HomeAfricaBBC2023 12 07Article 1894556

BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

Da wuya Matip ya sake buga wa Liverpool wasa a bana

Joel Matip Joel Matip

Da yiwuwar Joe Matip ba zai sake buga wa Liverpool wasa ba a wannan kakar, biyo bayan tabbacin da kocin ƙungiyar, Jurgen Klopp ya bayar na raunin da ɗan wasan ya ji a gwiwarsa.

Ɗan wasan bayan ya shiga wasan da Liverpool ta buga da Fulham a Anfield ranar Lahadi wanda aka tashi 4-3.

Bayan wasan ranar Laraba da Liverpool ta ci Sheffield 2-0, Kolpp ya tabbatar da cewa ɗan wasan na Kamaru mai shekara 32 ya samu rauni mai muni.

Dan wasan bayan dai na cikin shekararsa ta ƙarshe a kwataraginsa da Liverpool.

Matip ya koma Liverpool ne daga ƙungiyar Schalke ta Jamus shekaru bakwai da suka gabata, kuma ya buga mata wasa 201 a duka gasa, ya kuma zura kwallo 11.

"Wannan ba shi ne abin da nake tsammani ba, abun babu dadi" in ji Klopp. "Abubuwa na kasancewa haka a wasu lokutan. Amma dai babu dadi."