You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854014

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Da kyar idan Mbappe zai buga Champions League saboda rauni

Kylian Mbappe ya ji rauni Kylian Mbappe ya ji rauni

Kylian Mbappe ya ji rauni ranar Lahadi a wasan Ligue 1 da Paris St Germain ta yi nasara a kan Marseile.

Marseille ta yi rashin nasara a gidan PSG da ci 4-0 a wasan mako na shida a babbar gasar tamaula ta Faransa.

Dan kwallon tawagar Faransa ya yi kokarin ci gaba da buga wasan, bayan da ya yi karo da Leonardo Balerdi, inda daga baya aka sauya shi tun kafin hutun rabin lokaci.

Watakila Mbappe ba zai buga wa PSG gasar Champions League ba, wanda za ta ziyarci Newcastle United ranar 4 ga watan Oktoba.

Wadanda suka ci wa PSG kwallayen a ranar Lahadi:


  • Minti na 8 Achraf Hakimi
  • Minti na 37 Randal Kolo Muani
  • Minti na 47 Goncalo Ramos
  • Minti na 89 Goncalo Ramos

Da wannan sakamakon, PSG ta koma mataki na uku a kan teburin Ligue 1 da tazarar maki biyu tsakaninta da Brest, wadda ke jan ragama.

Marseille wadda a wannan karon aka doke ta karon farko a wannan kakar, tana ta bakwai a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da PSG.