You are here: HomeAfricaBBC2023 09 05Article 1838621

BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

Club World Cup: Man City za ta kara da Club Leon ko Urawa Reds

Hoton alama Hoton alama

Manchester City za ta fuskanci Club Leon ko kuma Urawa Reds a Club World Cup.

City ta samu gurbin shiga gasar a karon farko, bayan da ta lashe Champions League na kakar 2022-23.

Za kuma ta fara wasa ne a zagayen daf da na kusa da na karshe a gasar ta kofin zakarun nahiyoyin duniya.

Kungiyar Mexico, Club Leon ita ce ta lashe kofin Concacaf, yayin da Urawa Reds ta Japan ita ta dauki kofin zakarin nahiyar Asia.

Za a buga wasannin a Saudi Arabia tsakanin 12 zuwa 22 ga watan Disamba dauke da kungiyoyi bakwai.

Zakarun nahiyoyi shida ne ke buga gasar da kuma daya daga kasar mai masaukin baki, wato kungiyar da ta lashe kofin gasar kakar.

Sauran kungiyoyin sun hada da Al-Ahly ta Masar da Auckland City ta New Zealand daga Oceania da kuma Al-Ittihad ta Saudi Arabia, wadda ta lashe kofin babbar gasar kasar a 2022-23.

Sauran gurbi daya ya rage, bayan da ba a kammala Copa Libertadores ba tsakanin Boca Juniors da Palmeiras da Fluminense da kuma Internacional daga yankin Kudancin Amurka.

Wannan shine karo na 20 da za a gabatar da Fifa Club World Cup, kuma daga kakar nan za a sauya fasalin wasanni zuwa kungiyoyi 32 daga 2025.

A gasa 10 baya kungiyoyin nahiyar Turai ne ke lashe gasar da suka hada da Manchester United da Liverpool da Chelsea daga masu buga Premier League.

Real Madrid ce mai rike da kofin bara da ta ci Al-Hilal 5-3 a wasan karshe a birnin Rabat a Morocco.