You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824785

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Chelsea za ta ɗauki Caicedo kan fam miliyan 115 a matsayin mafi tsada a Birtaniya

Moises Caicedo Moises Caicedo

Chelsea ta amince za ta ɗauki ɗan kwallon Brighton, Moises Caicedo kan fam miliyan 115 a matsayin mafi tsada a Birtaniya.

Tun farko a ranar Juma'a Liverpool ta amince za ta sayi ɗan wasan mai shekara 21, ɗan ƙasar Ecuador fam miliyan 111.

To sai dai Caicedo ya zaɓi ya koma Chelsea, maimakon kungiyar Anfield.

Idan Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan kwallon za ta kara kafa wani tarihin da ta sayi Enzo Fernandez a Janairun kan fam miliyan 107.

Caicedo, wanda bai buga wa Brighton wasan Premier ranar Asabar da Luton ba, zai je Chelsea a auna koshin lafiyarsa.

Tun farko Brighton ta yi wa Caicedo farashin fam miliyan 100 a bana, bayan da Chelsea ta taya ɗan wasan karo biyu, amma ba a sayar mata da shi ba.

Ranar Lahadi Chelsea da Liverpool suka tashi 1-1 a wasan makon farko a Premier League a Stamford Bridge.