You are here: HomeAfricaBBC2023 01 30Article 1704761

BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

Chelsea ta taya Fernandez yuro miliyan 120

Graham Potter Graham Potter

Chelsea ta mika tayin yuro miliyan 120 ga dan wasan Benfica da Argentina, Enzo Fernandez.

Dama an shafe makonni Chelsea na son Benfica ta sakar mata dan wasan tsakiyar, da ya zama gwarzon matashin dan wasa a gasar kofin duniya ta Qatar 2022.

To amma kafin yanzu Benfica ta zargi Chelsea da raba hankalin dan wasan nata.

Idan har kungiyar ta Portugal ta aminta da sabon tayin, hakan na nufin Fernandez zai zama dan wasa mafi tsada a tarihin Premier League.

Kawo yanzu ba bu bayanan da suka nuna cewa Benfica za ta karbi wannan tayi.

A watan August ne Benfica ta sayi Fernandez daga River Plate kan fam miliyan 10.

Kuma tun zuwansa ya ci kwallo hudu a wasanni 29 da ya buga wa kungiyar tasa da ke Portugal.

Kazalika Fernandez ya ci wa kasarsa Argentina kwallo a gasar kofin duniya, lokacin da suka doke Mexico 2-0 a wasan rukuni.