You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836320

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Chelsea ta ɗauko Palmer daga Man City

Cole Palmer Cole Palmer

Chelsea ta sayi dan wasan gaban Ingila Cole Palmer daga Manchester City kan fam miliyan 40.

Yarjejeniyar ta haɗa da ƙarin £2.5m idan aka cika wasu sharudda kuma dan wasan mai shekara 21 ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru bakwai tare da zaɓin ƙarin shekara ɗaya.

Palmer yana cikin tawagar Ingila da ta lashe Gasar Cin Kofin Turai na 'yan ƙasa da shekara 21 a farkon wannan bazarar, kuma ya fara wasa ne a ɓangaren matasan City.

Palmer ya zura ƙwallo biyu a gasar cin kofin Uefa Super Cup da City ta doke Sevilla da kuma Community Shield da Arsenal ta doke su.

A baya kocin City Pep Guardiola ya ce ba za a bar Palmer ya tafi aro ba. West Ham ta yi sha'awar sayen shi a farkon wannan bazarar amma ana tunanin tayin aro kungiyar ta yi.