You are here: HomeAfricaBBC2023 01 11Article 1693631

BBC Hausa of Wednesday, 11 January 2023

Source: BBC

Chelsea ta ɗauki aron Joao Felix daga Atletico Madrid

Joao Felix Joao Felix

Ƙungiyar Chelsea ta ɗauki aron ɗan wasan gaba na Atletico Madrid Joao Felix zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.

An sha alaƙanta ɗan wasan mai shekara 23 da ƙungiyoyin Arsenal da kuma Manchester United, amma ya zaɓi zuwa Chelsea.

Ɗan wasan na ƙasar Portugal ya kuma tsawaita kwantaraginsa a Atletico zuwa 2027.

Chelsea na cikin manyan ƙungiyoyi a duniya kuma ina fatan taimaka mata cimma manufofinta," a cewar Felix.

"Ina matuƙar farin ciki da zuwana nan kuma cike nake murnar buga wasa a filin Stamford Bridge."

Atletico ta sayi Felix kan farashi na biyar mafi tsada a tarihi bayan ta biya Benfica fan miliyan 113 a lokacin da yake shekara 19 a 2019.

Ya zira ƙwallo 34 cikin wasa 131 da ya buga mata a dukkan gasanni, ya kuma bayar an ci ƙwallon 18.

Felix na cikin tawagar Portugal da ta buga Gasar Kofin Duniya a Qatar, har ma ya ci ƙwallo ɗaya a wasa biyar, inda ƙasarsa ta kai matakin 'yan 16.

A kakar wasa ta bana, Felix ya ci wa Atletico ƙwallo biyar kuma ya taimaka aka ci uku cikin wasa 20.