You are here: HomeAfricaBBC2023 04 12Article 1747934

BBC Hausa of Wednesday, 12 April 2023

Source: BBC

Chelsea na zawarcin Gavi, Liverpool na son dauko Mount, Newcastle na hararo Harvey

Wani dan kwallon Chelsea Wani dan kwallon Chelsea

Chelsea ta tattauna da ejan ɗin dan wasan tsakiya na Sifaniya Gavi, mai shekara 18, kan musayar shi ba tare da ko kwabo ba daga Barcelona a kakar wasanni. (AS - in Spanish)

Liverpool na da aniyar dauko dan wasan Chelsea Mason Mount, mai shekara 24, an fara batun dan wasan tsakiyar a kakar da muke ciki, bayan janyewa daga dauko dan wasan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund. (Football.London)

Bayern Munich na duba yiwuwar daukar dan wasan Napoli, kuma mai kai hari na Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 24, wanda ke son komawa bangaren Bundesliga. (Sky Germany - in German)

Tsohon kocin River Plate Marcelo Gallardo na son aikin dindindin a matsayin manajan kungiyar Chelsea. (UOL - in Portuguese)

Newcastle na sahun gaba a kulub-kulub na Premier League da suka shirya daukar dan wasan Harvey Barnes mai shekara 23. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Manchester City, daga Ireland ta Arewa Shea Charles, mai shekara 19, na cikin wadanda kungiyoyin Leeds, Brentford da Borussia Dortmund ke zawarci. (Guardian)

Real Madrid kuwa dan wasan gaba na Brazil Roberto Firmino, mai shekara 31 take muradi, idan kwanturaginsa da Liverpool ya kare a karshen kakar wasa. (El Nacional - in Spanish)

Idanun kungiyar West Ham na kan dan wasan Chelsea Conor Gallagher mai shekara 23, da dan wasan Manchester City Kalvin Phillips, mai shekara 27, wanda suke fatan zai maye gurbin ɗan ƙwallon tsakiya na Ingila Declan Rice, mai shekara 24. (Standard)

Arsenal na son dauko dan wasan tsakiya na kulob ɗin Flamengo, daga ƙasar Brazil, Matheus Goncalves mai shekara 17. (Sun)

Nottingham Forest ta tattauna da daraktan Rangers Ross Wilson kan batun wanda zai maye gurbin Filippo Giraldi. (Athletic )