You are here: HomeAfricaBBC2023 09 14Article 1844384

BBC Hausa of Thursday, 14 September 2023

Source: BBC

Chelsea na son Toney na Brentford, Juventus na kwaɗayin Partey daga Arsenal

Ivan Toney Ivan Toney

Chelsea ta nuna matsuwarta kan ɗan wasan Ingila Ivan Toney, wanda ke fuskantar dakatarwa na wata takwas kan karya dokokin hukumar kwallon kafa ta FA.

Matashin mai shekara 27 ba shi da damar buga wasa har sai ranar 17 ga watan Janairun 2023, amma yana iya dawo wa atisaye a wannan makon (football.london)

Juventus na duba yiwuwar miƙa tayinta ga ɗan wasan tsakiya a Ghana mai shekara 30 Thomas Partey domin maye gurbin Paul Pogba, mai shekara 30, wanda wataƙil a soke kwantiraginsa idan aka tabbatar da aikata laifin shan maganin kara kuzari. (La Repubblica - in Italian)

Ɗan wasan baya a Manchester United da Ingila Harry Maguire, mai shekara 30, na gab da komawa West Ham kan yarjejeniyar fam miliyan 30, a cewar kocin Hammers Kevin Nolan. (Talksport)

Tsohon ɗan baya a Liverpool da Ingila Glen Johnson ya ce ba zai yi mamaki ba idan Mohamed Salah, mai shekara 31, ya bar Anfield zuwa Saudiyya.

Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 150 da ƙungiyar Saudiyya ta Al-Ittihad ta gabatar kan ɗan wasan.(Liverpool Echo)

Ɗan wasan Nottingham Forest Jonjo Shelvey, mai shekara 31, na gab da komawa ƙungiyar Rizespor ta Turkiyya kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a ranar Juma'a.

Shelvey ya koma Forest ne daga Newcastle a wani kwantiragin shekara biyu da rabi a karshen watan Janairu.

Shi ma, ɗan wasan Forest din asalin Najeriya da ke buga gaba Emmanuel Dennis, mai shekara 25, na gab da barin ƙungiyar. (Telegraph - subscription required)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp, mai shekara 56, ya yi watsi da batun karbar ragamar tawagar Jamus bayan korar kociyarta Hansi Flick.

Dan ƙasar Jamus, Klopp, mai shekara 56, ke tafiyar da ragamar Liverpool tun 2015. (Sportschau)

Ƙungiyoyi a Turkiyya da Qatar sun shiga farauta yayin da Manchester United ke kokarin sakin ɗan wasanta na Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 26. (90min)

Sai dai, ana tunanin tsohon ɗan wasan na Ajax Van de Beek zai cigaba da zaman Old Trafford har watan Janairu. (Mirror)

Kungiyar Besiktas na son ɗauko aron dan wasan Manchester United asalin Turkiyya Hannibal Mejbri, mai shekara 20.

A ranar Juma'a za a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a Turkiyya. (Mirror)

Tsohon ɗan wasan Chelsea, mai kuma buga gefe a Belgium Eden Hazard na shirin rataye takalminsa yayinda ya cika shekara 32 bayan Real Madrid ta sake shi.(CaughtOffside - subscription required)

Tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter, mai shekara 48, ya ƙi amincewa da tayin da ya samu daga ƙungiyar Lyon ta Faransa da Rangers ta Scotland. (Sun)