You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829843

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Chelsea na shirin dauko sabon mai tsaron raga

Djordje Petrovic Djordje Petrovic

Chelsea na shirin kammala sayan mai tsaron gida Djordje Petrovic daga New England Revolution kan fam miliyan 12.5.

Dan wasan na Serbia mai shekaru 23 zai fafata da Robert Sanchez wurin samun matsayi na daya a Stamford Bridge.

Hakan na zuwa ne bayan Kepa Arrizabalaga ya bar kungiyar ya koma Real Madrid a matsayin aro yayin da Edouard Mendy ya kulla yarjejeniya da Al-Ahli.

Petrovic ya buga wasa 43 a gasar MLS da New England Revolution, kuma ya buga wa Serbia karawa biyu.

A halin yanzu golan Chelsea, Marcus Bettinelli yana jinya, yayin da Lucas Bergstrom mai shekaru 20 ya kasance a benci a wasa biyun da Mauricio Pochettino ya ja ragama a Premier Leaguee.

Chelsea ta kashe kusan fam miliyan 323 wajen sayo 'yan wasa takwas a wannan kasuwar cinikin.

Ta karya tarihin kashe kudi mafi yawa a lokacin bazara da kowane kulob a duniya ke kashewa - wanda ya zarce fam miliyan 292 na Real Madrid a shekarar 2019.

Sun kashe sama da fam miliyan 850 tun lokacin da Todd Boehly ya karbi ragamar mulkin kungiyar a bazarar bara.

A daren Juma'a ne Chelsea za ta kara da Luton a gida a gasar Premier, yayin da take neman samun nasarar farko a kakar bana.