You are here: HomeAfricaBBC2023 08 23Article 1830548

BBC Hausa of Wednesday, 23 August 2023

Source: BBC

Chelsea da Inter da Monaco na son daukar Balogun na Arsenal

Folarin Balogun Folarin Balogun

Chelsea da Inter Milan da Monaco na rige-rigen daukar dan kwallon Arsenal, Folarin Balogun.

Gunners ta yi wa dan kwallon mai shekara 22 farashin da ya kai fam miliyan 50, amma kawo yanzu Chelsea ba ta taya dan wasan ba.

An bayar da rahoton cewar Arsenal ba ta sallama tayin farko da Monaco ta yi kan dan kwallon ba, wanda Inter Milan ke bukata.

Dan wasan tawagar Amurka, ya taka rawar gani a wasannin aro da ya yi wa Reims, mai buga Ligue 1 da cin kwallo 22 a kakar da ta wuce.

A shirye Arsenal take ta sayar da dan kwallon idan aka taya shi da tsoka, domin Mikel Arteta bai sa dan kwallon cikin wadanda zai yi amfani da su ba.

Arsenal ba ta saka shi a wasa biyun da fara a gasar Premier ta bana ba, duk da Gabriel Jesus na jinya.

Eddie Nketiah ne yake buga gurbin, inda Gunners ta ci Nottingham Forest a ranar makon farko, sannan ta je ta ci Crystal Palace 1-0 ranar Litinin.