You are here: HomeAfricaBBC2023 09 19Article 1847303

BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

Chelsea da Bayern na zawarcin Ramsdale, Diaz zai koma Al Gharaf, Draxler kuma Al Ahli SC

Aaron Ramsdale Aaron Ramsdale

Chelsea da Bayern Munich na zawarcin Aaron Ramsdale, mai shekara 25, bayan dan wasan na Ingila kuma mai taka leda a Arsenal a matsayin gola, ya yi rashin nasara a wasan da Gunners da Everton a ranar Asabar. (Daily Mail)

Manchester United na shirin fara cinikin dan wasan gaba na Jamus, mai taka leda a Bayern Munich, Serge Gnabry inda kungiyar ta fara aje fam miliyan 52 akan dan wasan mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish)

Dan wasan baya na Uruguay mai taka leda a Atletico Madrid, Jose Maria Gimenez, mai shekara 28, na sha'awar komawa a Manchester United. (FourFourTwo)

Newcastle na duba yiwuwar taya dan wasan tsakiya na West Ham Lucas Paqueta, kan fam miliyan 52. An dai kuma fara rade-radin dan wasan mai shekara 26 na hararo kungiyar Manchester City a kakar wasannan, sai dai lamarin bai dore ba sakamakon binciken da ake yi akan sa kan zargin taka ka'ida ga dan Brazil din. (Daily Mail)

Da alama kungiyar Real Betis na zawarcin golan Sifaniya, David de Gea, 32, idan ya bar kungiyar Manchester United. (Fichajes, via Sun)

Mai tsaron baya na Faransa, Giulian Biancone, mai shekara 23, ya kammala dukkan abin da ya dace domin komawar dindindin kungiyar Olympiacos daga Nottingham. (The Athletic - subscription required)

Dan wasan Liverpool da Montevideo, Fabricio Diaz, mai shekara 20, zai koma kungiyar Al Gharafa ta Qatar, dan wasan tsakiyar na Uruguay ya yi matukar farin jini inda kungiyoyin Brighton da Barcelona suka nuna sha'awar daukarsa. (Fabrizio Romano)

Dan wasan tsakiya na Jamus, Julian Draxler, mai shekara 29, ya koma kungiyar Al Ahli SC ta kasar Qatar daga kungiyar Paris St-Germain kan kwantiragin dindindin. (Fabrizio Romano)

Mai tsaron gida na Ingila, da ke taka leda Chelsea Alfie Gilchrist mai shekara 19, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa watan Unin 2025. (Standard)