You are here: HomeAfricaBBC2021 04 03Article 1223467

BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: bbc.com

Chelsea 2 - 5 West Brom: Karon farko an doke Thomas Tuchel a Chelsea

Karon farko an doke Thomas Tuchel a matsayinsa na kocin Chelsea bayan West Bromwich Albion ta yi masa ci 5-2 a Stamford Bridge.

Chelsea ta ƙare wasan ne da ƴan wasa 10 bayan an ba Thiago Silva jan kati

Tuchel ya buga wasa 14 ba a doke shi ba a dukkanin wasannin da ya buga bayan Chelsea ta kori Frank Lampard a Janairu.

Ɗan wasan Chelsea Christian Pulisic ya fara ziyara ƙwallo a raga, kafin a ba Thiago jan kati.

Ana dab da zuwa hutun rabin lokaci ɗan wasan Albion Matheus Pereira ya ci ƙwallaye biyu.

Mbaye Diagne ya ci wa West Brom ƙwallo ta uku yayin da kuma Callum Robinson ya rufe da sauran ƙwallayen a ragar Chelsea.

Sakamakon wasan ƙalubale ne ga hamayyar da take na ƙare a huɗun farko domin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai.

Wannan ne karon farko da aka ci Chelsea ƙwallaye biyar tun 2011 da Arsenal ta zazzaga mata ƙwallayen.

Join our Newsletter