You are here: HomeAfricaBBC2021 04 27Article 1243648

BBC Hausa of Tuesday, 27 April 2021

Source: BBC

Champions League: Real za ta wasan daf da karshe na 30 a gasar Zakarun Turai

Yan wasan kungiyar Real Madrid Yan wasan kungiyar Real Madrid

Ranar Talata Real Madrid za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan farko na daf da karshe a Champions League na bana.

Wannan kuma shi ne wasa na 30 da kungiyar Spaniya za ta buga a karawar daf da karshe a gasar ta Zakarun Tuari, ita ce kan gaba a wannan bajintar.

Bayern Munich ce ta biyu mai yawan wasa 20 a karawar daf da karshe, sai Barcelona wadda ta kai wannan gurbin har karo 16.

Chelsea ita ce ta 16 daga cikin kungiyoyin da Real za ta fafata da ita a wannan gurbin, sai Bayern da ta hadu da ita sau bakwai.

Real ta yi tata burza da Barcelona sau uku a gasar zakarun Turai karawar daf da karshe.

Real Madrid ta lashe Champions League sau 13, ita kuwa Chelsea daya ne da ita da ta lashe a 2011/12.

Real Madrid da Chelsea sun kara a European Cup Winners Cup a 1971 inda Chelsea ta ci 2-1 a Ingila, sunnan suka tashi 1-1 a Spaniya.

A 1998 suka fafata a European Super Cup inda Chelsea ta yi nasara a kan Real Madrid da ci 1-0 ranar 28 ga watan Agusta.