You are here: HomeAfricaBBC2023 09 19Article 1847258

BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

Champions League: Man City ta fara da kafar dama a bana

Yan wasan Manchester City Yan wasan Manchester City

Manchester City ta fara kare kofinta ta hanyar doke Red Star Belgrade 3-1 a wasan farko cikin rukuni a Champions League a Etihad ranar Talata.

Daf da za su je hutu ne Red Stars ta ci ƙwallo ta hannun Osman Bukari, hakan aka kammala minti 45 din farko.

Minti biyu da komawa zagaye na biyu ne City ta farke ta hannun Julian Alvarez, wanda ya ƙara ƙwallo na biyu daga baya Rodrigo Hernandez ya ci na ukun.

Daya sakamakon wasan a rukuni na bakwai Young Boys ta yi rashin nasara a gida a hannun RB Leipzig da ci 3-1.

Ranar 4 ga watan Oktoba RB Leipzig za ta karɓi baƙuncin Manchester City a Jamus a karawa ta bi-biyu a rukuni na bakwai.

A bara, ƙungiyoyin sun kara a Champions League, inda suka tashi 1-1 a gidan Leipzig, sannan City ta ci 7-0.

Haka kuma ranar ta 4 ga watan Oktoba, Red Star Belgrade za ta karbi bakuncin Young Boys.

City ce ta lashe Champions League a bara kuma a karon farko, sannan ta dauki FA Cup da kuma Premier League.

Kungiyar ta Etihad ta kuma dauki Uefa Super Cup a bana, wadda ke shirin zuwa buga Fifa Club World Cup.