You are here: HomeAfricaBBC2023 07 06Article 1799333

BBC Hausa of Thursday, 6 July 2023

Source: BBC

Cesar Azpilicueta ya koma Atletico Madrid daga Chelsea bayan shekara 11

Kyaftin in Chelsea Cesar Azpilicueta ya kawo arshen zamansa a ƙungiyar bayan shekara 11 Kyaftin in Chelsea Cesar Azpilicueta ya kawo arshen zamansa a ƙungiyar bayan shekara 11

Kyaftin in Chelsea Cesar Azpilicueta ya kawo arshen zamansa a ƙungiyar bayan shekara 11, ya koma Atletico Madrid da ke Sifaniya.

Dan wasan mai shekara 33 ya lashe duk wata kyautar girmamawa da ake samu a Stamford Bridge, ciki har da Premeir biyu da Champions guda.

Azpilicueta na da sauran shekara ɗaya a Chelsea.

"Abu ne mawuya ci na bayyana yadda nake ji, amma dai daɗin ba zai musaltu ba," in ji shi.

Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Intenet cikin hawaye ɗan wasan ya ce "na bayar da komai da zan iya a wannan ƙungiya kuma ina sonta.

"Chelsea gida na ne, ina fatan dawowa ƙungiyar a wani matakin na daban." in ji shi.

Dan wasan ya fara kwallo ne yana yaro a Osasuna inda sannan ya yi shekara biyu a Marselle gabanin ya koma Chelsea fan miliyan 6.5 a watan Agustan 2012.

Ɗan wasan bayan ya ci kwallo 17 cikin wasa 508 da ya buga wa ƙungiyar ta yammacin Landan.

Cesar Azpilicueta na ɗaya daga cikin 'yan wasa shida da suka ci Premier da FA da League Cup da Champions da Uefa Super Cup da Fifa Club World Cup.