You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798562

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Carlo Ancelotti zai zama kocin Brazil a 2024

Carlo Ancelotti Carlo Ancelotti

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti zai karɓi ragamar horas da Brazil a 2024, in ji shugaban hukumar kwallon ƙafa ta ƙasar Ednaldo Rodrigues.

Ƙasar da ta lashe kofin duniya sau biyar ta yi amannar cewa ɗan ƙasar Italiyan shi ne ya fi dacewa da ya kai Brazil Copa America da za a yi a watan Yunin 2024.

Rodrigues ya ce kocin Fernando Diniz zai ci gaba da lura da ƙungiyar ta Brazil da ake kira Selacao tare da ci gaba da aikinsa na horar da Flumine.

"Shi ne zai miƙa wa Ancelotti ragamar Brazil," in ji Rodrigues.

"Salon wasansa ya yi kusa da na kocin da zai karɓi aikin kai ƙungiyar Copa America, Ancelotti.

"Ba za mu kira shi kocin riƙon kwarya ba ga tawagarmu ta ƙasa."

Brazil ba ta da koci tun bayan kammala gasar kofin Duniya da aka kammala a bara, lokacin da Tite ya ajiye aiki bayan cire ƙasar da Croatia ta yi a wasan kusa da daf da na ƙarshe.

Kocin da ke jan ragamar tawagar 'yan ƙasa da shekara 20 ne ke lura da Brazil a wasanni sa da zumunta da take yi a kwanakin nan.

Kocin mai shekara 64 ya koma Bernabeu ne a 2021 bayan ya bar Everton, kuma tun bayan komarwarsa ya ci Champions da La Liga da Copa del Rey da sauransu.

Da kofin zakarun Turai da ya lashe a 2022 a wasan ƙarshe a hannun Liverpool, Ancelotti ya lashe kofin nahiyar Turai na huɗu kenan a matsayinsa na koci, na biyu a REal Madrid bayan biyu da ya lashe a AC Milan.