You are here: HomeAfricaBBC2023 09 05Article 1838609

BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

Carabao Cup: An tsayar da ranar wasan Brentford da Arsenal

File foto File foto

An tsayar da ranar karawa a Carabao Cup fafatawar zagaye na uku tsakanin Brentford da Arsenal zuwa 27 ga watan Satumba.

Karon farko da za su kara a kofin tun bayan 2018, bayan da Gunners ta ci 3-0 a Emirates.

Sannan Arsenal ta ci 3-0 a gidan Brentford a Satumbar 2022 a Premier League, inda William Saliba da Gabriel Jesus da kuma Fabio Vieira suka ci mata kwallayen.

Ranar 11 ga watan Fabrairu, Arsenal da Brentford suka tashi 1-1 a Emirates, inda Leandro Trossard ya fara cin kwallo Ivan Toney ya farke.

Arsenal tare da kungiyoyi bakwai da za su buga gasar Zakarun Turai sun shiga wasannin Carabao Cup a zagaye na uku ne.

Gunners na fatan daukar kofin a karo na uku, bayan da ta lashe a 1986/87 da kuma 1992/93.

Arsenal, wadda take ta biyar a teburin Premier League ta hada maki 10, yayin da Brentford take ta shida a teburin mai maki takwas.