You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829081

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Calvert-Lewin zai yi jinya bayan karya mukami

Dominic Calvert-Lewin Dominic Calvert-Lewin

Dominic Calvert-Lewin zai kara yin jinya, bayan da ake cewar ya karya mukami a wasan Premier League da Aston Villa ta ci Evrton 4-0 ranar Lahadi.

Calvert-Lewin, mai shekara 26, an canja shi a minti na 38 da take leda, bayan da ya yi karo da golan Villa, Emiliano Martinez.

Ma'aikatan lafiyar kungiyar za su sake auna koshin lafiyarsa daga nan su bayar da shawara kan abin da ya kamata.

Tun farko Calvert-Lewin ya yi yunkurin ci gaba da wasan, to amma dole ya hakura aka fitar dashi.

Bayan kammala wasan koci, Sean Dyche ya yi fatan raunin kada ya zama mai muni, domin yana bukatarsa a sauran wasannin da ke gabansu.

Calvert-Lewin, wanda ya yi fama da jinya a bara da cin kwallo biyu a kacokan din kakar, kuma kwallo hudu ya ci a League jimilla tun daga Agustan 2021.

Wasa hudu ya yi minti 90 a Everton tun da fara kakar da ta wuce da daya a watan Janairu.