You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716398

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

CBN ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin naira 1,000 da 500

Tsohon naira Tsohon naira

Babban Bankin Najeriya ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000 da 500 waɗanda yawansu bai zarta N500,000 ba.

Bankin na CBN ya bayyana haka ne a yau Juma’a, bayan koke-koken da ake ta samu a faɗin ƙasar kan wahalar da al’umma ke fuskanta wajen samun sababbin kuɗin.

Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC da wannan bayani.