You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854032

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

CAF ta sanar da ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar 2025 da 2027

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afrika - CAF Patrice Motsepe Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afrika - CAF Patrice Motsepe

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afrika - CAF Patrice Motsepe ya sanar da ƙasashen da za su ɗauki baƙuncin gasar cin kofin ƙwallon Afrika, Afcon a shekara ta 2025 da kuma 2027.

An sanar cewa Moroko ita ce wadda za ta karɓi baƙuncin gasar a 2025.

Wannan ne karo na biyu da za a buga gasar a ƙasar, wadda ta taɓa karɓar baƙuncin ta a shekarar 1988.

Ƙasashe kamar Algeriya da Zambia da Benin da kuma Najeriya ne suka janye wa Moroko.

Har wa yau Moroko ɗin na takarar ɗaukar baƙuncin gasar cin kofin duniya a 2030.

Hukumar ta Caf ta kuma sanar cewa Kenya da Tanzania da kuma Uganda za su haɗa gwiwa domin ɗaukar baƙuncin gasar a shekarar 2027.

Rabon da a buga gasar a gabashin Afrika tun a shekarar 1976 lokacin da Habasha ta dauki bakunci.

A ranar 13 ga watan Janairun 2024 ne za a buga gasar Afcon ta 2023 a ƙasar Ivory Coast.