You are here: HomeAfricaBBC2023 02 19Article 1717364

BBC Hausa of Sunday, 19 February 2023

Source: BBC

Busquets zai buga wasan Barca da Cadiz a La Liga

Sergio Busquets Sergio Busquets

Barcelona za ta karbi bakuncin Cadiz a wasan mako na 22 a La Liga a Nou Camp ranar Lahadi.

Tuni Barcelona ta bayyana kyaftin, Sergio Busquets cikin wadanda za su fuskanci Cadiz a karawar ta La Liga.

Kyaftin din ya ji rauni ranar 5 ga watan Fabrairu a wasan La Liga da Barcelona ta ci Sevilla 3-0.

Wasa biyu ne Busquets bai yi wa Barcelona ba, shine wanda ta je ta ci Villareal 1-0 a La Liga da wanda ta yi 2-2 da Manchester United ranar Alhamis.

Cikin Satumbar 2022, Barcelona ta je Cadiz ta ci 4-0 a karawar ta babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Sai a bara Cadiz ta ci Barcelona 1-0 ranar 18 ga watan Afirilun 2022 a La Liga.

'Yan wasa 22 da za su fuskanci Cadiz:

Ter Stegen, Sergio, Gavi, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Christensen, Marcos Alonso, Jordi Alba da kuma Kessie

Sauran sun hada da S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Pablo Torre, Arnau Tenas A. Alarcón da kuma Sergio Busquets.