You are here: HomeAfricaBBC2023 02 23Article 1720073

BBC Hausa of Thursday, 23 February 2023

Source: BBC

Bukayo Saka zai ci gaba da taka leda a Arsenal

Bukayo Saka Bukayo Saka

Dan wasan tawagar Ingila Bukayo Saka, da ke Arsenal, wadda take ta daya a Premier a bana na tattaunawa kan tsawaita zamansa a Emirates.

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Gunners da dan wasan, amma ba a kai ga cimma matsaya kan sabuwar yarjejeniyar da za a gabatar masa ba.

Saka, mai shekara 21 yana daga cikin fitattun 'yan wasan Arsenal, wanda ya ci kwallo tara ya bayar da takwas aka zura a raga a wasa 23 a kakar nan.

Kwantiragin dan wasan zai kare a karshen kakar 2024, wanda ya fara Arsenal daga makarantar kungiyar.

Ya fara yi wa Gunners tamaula a Nuwambar 2018.

Ana sa ran za a gabatar masa da yarjejeniyar fam miliyan 10 duk shekara da za ta kare a 2028, bayan da Arsenal ke fatan daukar Premier a karon farko tun bayan kusan shekara 20.

Dan wasan tawagar Brazil, Gabriel Martinelli, mai shekara 21, ya tsawaita zamansa a Emirates a cikin Fabrairu.

Kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama, wadda take ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City za ta ziyarci Leicester City ranar Asabar.