You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817387

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Buffon ya yi ritaya daga taka leda

Tsohon golan Italiya, Gianluigi Buffon Tsohon golan Italiya, Gianluigi Buffon

Tsohon golan Italiya, Gianluigi Buffon ya yi ritaya daga tamaula yana da shekara 45 da haihuwa.

Ya sanar a kafar sada zumunta; ''Na kawo karshen tamaula. Kun nuna min goyon baya, na yi muku abin da kuke sha'awa. Tare muka yi wasannin.''

Buffon ya kawo karshen shekara 28 yana sana'ar tamaula, wanda ya lashe kofin duniya a 2006.

Mai tsaron ragar ya dauki Serie A 10 a Juventus da kofin Ligue 1 a Paris St Germain.

Ya karasa wasannin a kungiyar da ya fara yi wa tamaula yana matashi a 1995 a Parma, wadda take buga gasar Serie B.

Buffon, wanda yake da sauran kwantiragi da Parma zuwa karshen 2024, ya buga mata karawa 19, wanda ke fama da jinyar raunuka.

Ya fara taka leda a Parma daga makarantar horar tamaular kungiyar, wadda ya fara ji wa Serie A a Nuwambar 1995.

Daga nan ya koma Juventus a 2001, kungiyar da ya yi mata wasanni da yawa daga baya ya koma PSG a kakar 2018-19.

Ya yi karawa 657 a babbar gasar tamaula ta Italiya, kuma shi ne kan gaba a yawan buga wasanni, wanda ya tsare ragar tawagar Italiya sau 176.