You are here: HomeAfricaBBC2021 05 04Article 1250707

BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: BBC

Bill da Melinda Gates: Manyan attajiran duniya shida da aurensu ya mutu

Jeff Bezos, mutumin da ya ƙirƙiri kamfanin Amazon ma ya rabu da matarsa Mackenzie a shekarar 2019 Jeff Bezos, mutumin da ya ƙirƙiri kamfanin Amazon ma ya rabu da matarsa Mackenzie a shekarar 2019

Aure wani muhimmin jigo ne a rayuwar kowane bangare na halitta wanda ta hanyarsa ne al'umma ke yaduwa.

Sai dai a duk lokacin da aure ya mutu, hakan yana taɓa zukatan jama'a.

Haka lamarin yake idan aka ce auren wasu mashahurai ko attajirai ya mutu a duniya - lamarin na jan hankalin al'umma har ta kai an samar da maudu'i a shafukan sada zumunta musamman a Tuwita domin tattauna abin.

Hakan ne ya sa labarin rabuwar auren Bill da Melinda Gates ya ja hankalin duniya, lamarin da har yanzu yake cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafukan intanet.

Baya ga mutuwar auren Bill da Melinda Gates, akwai wasu manyan attajirai da su ma a baya aurensu ya mutu. Ga wasu daga cikinsu:

1. Bill Gates

A ranar Litinin ne Bill da Melinda Gates - ma'auratan da suka samar da gidauniya mafi karfin arziki a duniya - suka sanar da raba aurensu bayan shekara 27 suna tare.

A wata sanarwar hadin gwiwa, attijiran biyu sun ce matakin ba zai shafi harkokin gidauniyar da suke tafiyarwa tare ba.

Sun hadu ne a shekarun 1980 lokacin da Melinda ta soma aiki a kamfanin Microsoft mallakin Bill. Ma'auratan sun haifi 'ya'ya uku.

Mr Gates - wanda tsohon shugaban kamfanin Microsoft da ya kafa - na daya daga cikin manyan attijiran duniya.

A shekarar da ta gabata ya sanar da cewa zai bar mukamin da yake rike da shi a katafaren kamfaninsa na Microsoft domin mayar da hankali kan ayyukan agaji.

Bill Gates shi ne mutum na hudu mafi arziki a duniya, a cewar mujallar Forbes kuma ya mallaki $124bn (£89bn).

2. Jeff Bezos

Baya ga mutuwar auren Bill da Melinda Gates, Jeff Bezos, mutumin da ya ƙirƙiri kamfanin Amazon ma ya rabu da matarsa Mackenzie a shekarar 2019 bayan shafe shekara 25 suna tare.

Bezos - mai shekara 56 wanda ya mallaki $136.2bn - na ɗaya daga cikin attajiran duniya. Kamfaninsa na Amazon shi ne ke da kashi 95 cikin 100 na dukiyar da ya mallaka.

Shi ne kuma ya mallaki Jaridar Washington Post da Kamfanin Blue Origin. Mutuwar aurensu ta sa matarsa yar shekara 50 zama mace ta uku mafi arziki a duniya.

3. Alec Wildenstein

Kafin duniya ta san da batun rabuwar auren Bezos, attajiri Alec Wildenstein ya rabu da mai dakinsa Jocelyn Wildensteina 1999.

Alec Wildenstein dan asalin Faransa ne da ke zaune a Amurka kuma fitaccen ɗan kasuwa da ya shahara a zane-zane.

Ya saki matarsa da suka shafe shekara 21 suna tare.

Rabuwarsu ta sa matar za ta riƙa samun maƙudan kuɗi har $100m kowace shekara har tsawon shekara 13 - ƙididdigar kuɗin ta kai $3.8bn

4. Bill Gross

Ɗaya daga cikin mutuwar auren da ta ja hankalin al'umma da ba ta zo ta daɗi ba ita ce ta ma'aurata Bill da Sue Gross. Bill Gross da ke da hannun jari kuma manajan kamfanin Pimco.

Sue Gross ta gabatar da takardar saki a cikin 2016 kuma a 2017, ta samu maƙudan kuɗaɗe har da mallakar gida a Laguna da aka ƙiyasta kuɗinsa kan $36m da kuma wani zane da ta siyar kan irin wannan adadin.

Bill ya nemi ya ɗauki ɗaya daga cikin magen da suke kiwo guda uku amma kuma hakan bai samu ba inda a ƙarshe matar ce ta samu izinin kula da magunan.

Bayan haka kuma, Bill ya rasa matsayinsa a mujallar The Forbes a 2018, bayan ya kasance cikin jadawalin masu arzikin duniya fiye da shekara 14 da suka gabata.

5. Rupert Murdoch

Mashahurin attajirin nan Rupert Murdoch da matarsa ƴar jarida Anna Torv su ma sun raba-gari a aurensu na shekara 31 da suka samu yara uku.

Sai dai sun yanke shawarar rabuwa bayan da Murdoch ya yi ritaya daga aikin jarida. Lokacin da ya sanar da ajiye aiki a 1998, ma'auratan suka yanke shawarar raba aurensu a 1999.

Wasu rahotanni sun ce Anna Torv ta samu arzikin $1.7bn sakamakon rabuwarsu sai dai bayanai sun nuna cewa kwana 17 tsakani, Murdoch ya auri Wendy Denn yayin da ita kuma Torv ta auri William Mann bayan wata shida da rabuwa da mijinta na farko.

6. Elon Musk

Attajirin nan Elon Musk, mai kamfanin Tesla da SpaceX ya karaɗe shafukan sada zumunta a 2008 lokacin da ya saki matarsa ta farko Justine Musk.

Rahotanni sun ce ba a kotu aka yi rabon dukiyar ba sannan dukkansu za su rika kula da yaransu biyar.

Jim kaɗan da rabuwarsu da Justice, Elon ya fara soyayya da Talulah Riley a 2008. Elon da Talulah sun yi aure a 2010 amma kuma bayan shekara biyu ne suka rabu.

A 2013 kuma suka sake ɗinkewa sai dai kuma sun sake komawa gidan jiya bayan shekara daya da sake auren.

Sun kammala batun sakin nasu a 2016 kuma bayan nan rahotanni sun ce Elon ya yi soyayya da fitattun mata irinsu Cameron Diaz da Amber Heard kuma a yanzu yana tare da mawaƙiyar nan ƴar California Grimes.