You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809536

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Bidiyon matan da aka yi wa tsirara a Indiya na neman tayar da hargitsi

Sojojin Ukraine Sojojin Ukraine

Wani bidiyo da ya nuna wasu matasa sun tasa wasu mata tsirara a gaba suna dukan su a yankin arewa maso gabashin Manipur da ke Indiya, na neman haifar da rikici a faɗin ƙasar.

Yan sanda sun ce sun gurfanar da ɗaya daga cikin waɗanda aka gani a bidiyon, sun ce kuma suna fatan damƙe sauran matasan nan bada jimawa ba.

A ranar Alhamis, majalisar ƙasar ta nemi a yi muhawara a kan batun, sai dai ƙudurin ya gamu da cikas.

Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya ce lamarin ya kunyata Indiya a idon duniya, kuma in ji shi, ba za a sassautawa duk waɗanda ke da hannu a lamarin ba.

"Ina mai tabbatarwa yan ƙasa cewa doka za ta yi aikinta, kuma abin da ya faru da matan Manipur ba abu ne da za a taɓa mantawa da shi ba." in ji shi, daga bisani dai ya kawo ƙarshen shirun da ake zargin ya yi a kan lamarin, bayan kwashe tsawon wata biyu da faruwar lamarin a Manipur.

Alƙalin alƙalan India DY Chandrachud shi ma ya nuna damuwarsa a kan cin zarafin, ya kuma ce "kotun ƙoli ta kaɗu da ganin bidiyon".

Ya ce "idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, mu za mu ɗauka."

Gargaɗi: Wannan labarin na ƙunshe da bayanai waɗanda za su iya tayar da hankali.

Ƴan sanda sun ce an ci zarafin matan ne tun ranar 4 ga watan Mayu, amman sai ranar Alhamis ɗin da ta wuce ne lamarin ya bayyana saboda bidiyon da ya yi ta yaow a shafukan sada zumunta.

Gwamnatin Indiya ta umarci kamfanonin sada zumunta su goge bidiyon daga shafukansu.

Aƙalla mutum 130 ne suka rasu, wasu 60,000 suka rasa muhallansu saboda rikicin ƙabilanci da aka fara a watan Mayu tsakanin ƴan ƙabilar Meitei da Kuku a Manipur.

Bidiyon mai cike da tashin hankali wanda ya nuna wasu mata biyu tsirara, ana cin zarafin su, ya karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Laraba.

An ga wasu matasa na jan su da ƙarfin tuwo, inda daga bisani suka ingiza su wani fili.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar shugabannin ƙabilar yankin ta ce an yi ta'asar ne a wani ƙauye da ke gundumar Kangpokpi, kuma an aikata hakan ne ga matan ƙabilar Kuki-Zo, har ma ana zargin an yi masu fyaɗe.

Bai kamata haka ta faru a sabuwar Indiya ba

Abu ne sananne cewa, jikin mata ya zama wani abu da akan yi amfani da shi lokacin zanga-zanga ko rikici, kuma ana amfani da fyaɗe da cin zarafin mata a matsayin wani makami a lokacin rikici.

Cin zarafin matan ƙabilar Kuki a Manipur wani babban misali ne na baya-bayanan da ke tabbatar da hakan.

Bidiyon ya nuna matan na kuka suna kururuwa cikin tsananin azaba, kuma sun riƙa roƙon matasan a kan su kyale su, abin gwanin tashin hankali.

Gaskiyar lamari shi ne, duk da hukumomi sun ce sun kama mutum ɗaya a cikin waɗanda ake zargin sun aikata laifin, hakan bai ba da ƙwarin gwiwar cewa ko hukumomi za su yi abin da ya dace kan lamarin ba, kasancewar bidiyon ya nuna fuskokin matasa da dama amma a cikin wata biyu a ce mutum ɗaya kawai aka iya kamawa.

Sai dai ɓacin ran da ya biyo bayan fitowar faifan bidiyon a Indiya ya sa an fara hasashe kan munanan laifukan da ake aikatawa a ƙasar.

Har ila yau, hakan ya janyo dasa ayar tambaya a kan gwamnatin Indiya, yayin da hakan ya tilasta Firaminista Modi yin jawabi a kan rikicin ƙabilancin da jihar Manipur ke fuskanta.