You are here: HomeAfricaBBC2023 06 06Article 1781315

BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

Benzema ya koma Al-Ittahad in ji wata majiya daga kungiyar

Karim Benzema Karim Benzema

Karim Benzema ya koma Al-Ittihad kan yarjejeniyar kaka uku, in ji wata majiya daga ƙungiyar ta Jeddah, wadda ta sanar da kamfanin dillacin labarai na AFP.

Ranar Lahadi Real Madrid ta sanar cewar tsohon ɗan wasan Faransa mai shekara 35 zai bar Santiago Bernabeu, bayan shekara 14 da ya yi a Sifaniya.

Idan har ta tabbata cewa Benzema ya koma Saudi Arabia, to zai taka leda tare da tsohon dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai wasa a kungiyar Al Nassr.

Ronaldo ya koma Saudi Arabia da taka leda daga Manchester United a watan Janairun 2023, bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar.

Ana alakanta Lionel Messi da cewar shima zai koma taka leda a gasar ta gabas na tsakiya, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris Saint-Germain a karshen kakar nan.

Manyan jami'an Al Hilal ta Saudi Arabia sun je Faransa, domin kulla yarjejeniya da Messi, in ji wata majiya da ta sanar da AFP.

Benzema ya koma Real Madrid a 2009 daga kungiyar Lyon mai buga Ligue 1.

Ya buga wa Real wasa 648 da cin kwallo 354, shine na biyu a yawan ci wa kungiyar kwallaye a tarihi, bayan Ronaldo.

Tsohon dan wasan tawagar Faransa, ya lashe Champions Leagues biyar da La Liga hudu da Copa del Rey uku a Real Madrid.

Bayan da dan wasan ya ja ragamar Real Madrid a 2021-22 da ta lashe Champions League ya kuma dauki Ballon d'Or, daga nan ya yi ta jinya da ta hana shi buga wa kasarsa kofin duniya a Qatar.

Benzema ya yi ban kwana da Real Madrid ranar Talata.

Kawo yanzu Saudi Arabia ta lissafa 'yan wasa 10 fitattu da take son su buga gasarta nan gaba, wadanda ko dai sun ci Champions League ko sun dauki kofin duniya.

Cikin 'yan kwallon har da Luka Modric na Real Madrid da golan Tottenham, Hugo Lloris da , N'Golo Kante na Chelsea, wadanda kwantiraginsu ke daf da karewa.

Ita dai Saudi Arabia na fatan samun izinin karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2030 ko kuma 2034, domin ta bunkasa tamaula a fadin kasar.