You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837790

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Bellingham ya ci kwallo na biyar a wasa huɗu a jere a La liga

Jude Bellingham Jude Bellingham

Real Madrid ta lashe dukkan wasa huɗun da fara La Liga ta bana, bayan da ta doke Getafe 2-1 ranar Asabar.

Minti 11 da fara wasa ne Getafe ta ci kwallo ta hannun Borja Mayoral, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Real ta farke ta hannun Joselu.

Daf da za a tashi Jude Bellingham, wanda ya koma Real a bana daga Borussia Dortmund ya ƙara na biyu.

Dan wasan tawagar Ingila ya ci kwallo na biyar a wasa huɗun da ya buga wa Real Madrid da fara kakar bana.

Bellingham ya fara ci wa Real kwallo a karawar da ta je ta ci Athletic Bilbao 2-0, bayan da Rodrygo ya fara cin ta farko ranar 12 ga watan Agusta.

Ranar 19 ga watan Agusta Real ta je ta ci Almeria 3-1, inda Bellingham ya ci biyu daga ciki.

Bellingham ne ya ci wa Real kwallo tilo da ta zura a ragar Celta Vigo a wasan mako na uku a La Liga ranar 25 ga watan Agusta.

Yanzu dai Real Madrid ta cinye dukkan wasa hudu da ta buga da fara gasar La Liga ta bana, wadda Barcelona ce ke rike da kofin bara.

Ranar 17 ga watan Satumba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Sociedad a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.