You are here: HomeAfricaBBC2023 08 27Article 1832825

BBC Hausa of Sunday, 27 August 2023

Source: BBC

Bellingham ne kan gaba a cin kwallaye a La Liga a 2023/24

Jude Bellingham Jude Bellingham

Real Madrid ta lashe dukkan wasa uku da ta buga tun bayan fara La Liga a kakar nan, ciki har da wanda ta je ta doke Celta Vigo 1-0 ranar Juma'a 25 ga watan Agusta.

Sabon dan wasan da Real ta dauka a bana Jude Bellingham ne ya ci mata kwallo sauran minti tara a tashi daga karawar.

Kawo yanzu dan wasan tawagar Ingila ya zura kwallo hudu a raga a wasa uku da ya buga wa Real Madrid karawa uku da fara babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Real ta fara wasa da bude La Liga da cin Bilbao 2-0 ranar 12 ga watan Agusta, inda Rodrygo ya fara cin kwallo, sannan Jude Bellingham ya kara na biyu.

Ranar 19 ga watan Agusta Real Madrid ta je ta doke Almeria 3-1 a wasan mako na biyu a La Liga.

Almeria ce ta fara cin Real Madrid a minti uku da take leda ta hannun Sergio Arribas, sai dai minti 16 Bellighma ya farke kwallo.

Bayan da suka koma hutu a zagaye na biyu ne Real ta kara na biyu ta hannun Bellingham, sannan Vinicius Junior ya kara na uku.

Bellingham, wanda ya zura kwallo hudu daga karawa uku a La Liga ya koma Real Madrid daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 88.5.

Ranar Asabar Real Madrid za ta karbi bakuncin Getafe ranar 2 ga watan Satumba a wasan fafatawar mako na hudu.

Sakamakon wasannin La Liga uku da Real Madrid ta buga a bana:

Asabar 12 ga watan Agusta 2023


  • Ath Bilbao 0 - 2 Real Madrid

Asabar 19 ga watan Agusta 2023


  • Almeria 1 - 3 Real Madrid

Juma'a 25 ga watan Agusta 2023


  • Celta Vigo 0 - 1 Real Madrid