You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853942

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Begen Kogin Nilu da rayuwar mutanen da yaƙin Sudan ya ɗaiɗaita

Mohamed Osman ya koma ƙasarsa ta haihuwa, Sudan Mohamed Osman ya koma ƙasarsa ta haihuwa, Sudan

Wakilin sashen Larabci na BBC, Mohamed Osman ya koma ƙasarsa ta haihuwa, Sudan, karon farko tun bayan tilasta masa tserewa lokacin ɓarkewar yaƙi a watan Afrilu, kuma ya bayyana yadda abubuwa suka sauya a ƙasar.

"Bayan komawa gida cikin wata biyar da barin mahaifata, iska, zafi da kuma ɗumi na birnin Port Sudan sun dawo sabbi a fuskata."

Daga ƙarshe dai na koma gida - ba baƙon-haure ko ɗan gudun hijira a wata ƙasa ba, musamman ma Masar - ƙasar da mu ƴan Sudan, ke da kyakkyawar alaƙa da ita.

Yawancin mutane daga waɗannan ƙasashe biyu, suna magana ne da harshe iri ɗaya, abinci iri ɗaya, addini ɗaya - har ma ta kai suna amfani da ruwan kogi ɗaya wato Kogin Nilu.

Sai dai ba gida ba ne.

Wata dattijuwa, wadda muke cikin jirgi ɗaya, ta fi kowa nuna farin ciki, ta yi ta kukan murna lokacin da kafarta ta taka Sudan, yayin da take tunawa fa yadda ta tafi Masar don yin jinya - Sai dai ta maƙale a can lokacin da Sudan ta auka cikin yaƙin basasa a watan Afrilu.

An fara yaƙin ne bayan saɓanin da ya shiga tsakanin manyan janar-janar ɗin ƙasar biyu - Shugaban mulki soji, Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohamed Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.

Na kawo ziyara ta taƙaitaccen lokaci a Port Sudan, yayin da yaƙi yake ci gaba da ɗaiɗaita Omdurman, mahaifata. Ina jin ciwon rashin komawa gida.

Omdurman ya kasance gari ne mai tarin rikice-rikice, inda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da wani abokina wanda harsashi ya faɗa gidansa lokacin da yaƙi ya ƙazance tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF na janar Dagalo.

Matar da muka haɗu a jirgi kuwa, ta dawo bakin gaɓa, mahaifarta - da ke jihar Gezira - na cikin kwanciyar hankali a yanzu.

Mun shiga jirgin ne da muka shafe tsawon sa'a biyu daga Alƙahira, babban birnin Masar zuwa Port Sudan. Shi ne jirgin farko da ya ɗauko fasinjoji zuwa Sudan tun bayan ɓarkewar yaƙi.

Filin jirgin saman Port Sudan kaɗai aka buɗe. Sauran duk a rufe suke - ciki har da filin jiragen sama na ƙasashen duniya da ke Khartoum, babban birnin ƙasar, saboda shi ma birnin ya fuskanci artabu tsakanin dakaru da harbin makaman atilare da sauransu kamar dai Omdurman a faɗin Kogin Nilu.

A yanzu ana samun zirga-zirgar jiragen sama kowacce rana zuwa Port Sudan, yawanci sun kasance tsofaffi ne a ciki, waɗanda suke komawa garuruwansu da faɗa bai ɗaiɗaita ba.

Masu ƙaramin ƙarfi da matasa ƴan Sudan na komawa gida cikin motocin bas da ke barin Masar a kullum. Wasu lokutan sukan shafe kwana uku a hanya kafin isa gida, saboda Sudan tana da faɗin gaske, kuma ba ta da tituna masu kyau.

Sun yi rayuwa cikin wahala a Masar, saboda Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta tanadar da sansanoni da kuma abinci ba - saɓanin Chadi, wadda ke ɗauke da ƴan gudun hijirar Sudan, da suka kai 420,000. Yayin da Masar ke da aƘalla mutum 320,000, a cewar alƙaluma.

Na shafe mako biyu a Port Sudan, wanda ya dawo babban birni ga Sudan na wani lokaci, yaƙin ya tilasta wa Janar Burhan komawa birnin ganin dakarun RSF ne ke iko da yawancin wurare a Khartoum, ciki har da gine-ginen gwamnati masu muhimmanci.

An yi masa ƙawanya a hedkwatar sojoji da ke Khartoum tun soma yaƙin har zuwa watan Agusta, bayan ya samu damar ficewa. Dakarun RSF sun ɗauki tsawon lokaci suna kai munanan hare-hare da zimmar karɓe iko da ginin.

Ana fargabar cewa yaƙin zai yi sanadin kafa gwamnatoci biyu a Sudan masu gaba da juna - ɗaya a ɓangaren Janar Dagalo a Khartoum, yayin ɗayar kuma a wurin Janar Burhan a Port Sudan.

Ministocin janar Burhan - ko kuma waɗanda ya zaɓa - su ma sun koma zama a Port Sudan, inda ma'aikatar harkokin waje ta buƙaci hukumomin birnin su ba ta fili domin ta gina hedkwatarta.

Ofisoshin jakadancin ƙasashe da dama har da na Majalisar Ɗinkin Duniya su ma sun koma Port Sudan - birni mai muhimmanci da ke kusa da Tekun Maliya.

Duk da yake akwai zaman lafiya a birnin, amma an gwabza faɗa cikinsa a makon da ya gabata, lokacin da sojojin gwamnati suka yi ƙoƙarin cire shingayen tsaro da wasu mayaƙa suka kafa.

Hakan dai ya haifar da fargabar cewa yaƙin na iya bazuwa cikin birnin, amma kawo yanzu dakarun gwamnati sun ci gaba da riƙe madafun iko, suna gudanar da sintiri tare da aiwatar da dokar hana fita daga ƙarfe 11:00 zuwa ƙarfe 06:00.

A yanzu haka, ana katse wutar lantarki na sa’o’i da dama a kullum, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwa da gidaje yin amfani da janaretocin da suka ta’azzara gurɓacewar iska da hayaniya a birnin na gaɓar teku, wurin da ake yawan zuwa hutu kafin ɓarkewar yaƙi.

Port Sudan wanda da ya kasance birnin da abokai da masoya suka saba haɗuwa a kowanne lokaci har daddare - yanzu ba haka abin yake ba saboda yaƙin.

Mai gidan abinci, Ibrahim Taha, ya ce an tilasta masa rufe kasuwancinsa, saboda tsadar farashi yayin da abokan cinikinsa suka ragu.

Yanzu ba shi da aikin yi.

Wani mai gidan abincin, wanda ya ƙware wajen sarrafa "al-Aqashi", sanannen abinci ne na gasasshen nama ya ce yaƙin ya tilasta masa rufe kasuwancinsa a Khartoum, kuma ya yi ƙaura zuwa Port Sudan.

“Na yi asara mai yawa a birnin Khartoum, bayan ƙungiyar RSF ta karɓe iko da unguwar al-Amarat, inda gidan cin abincina yake, don haka na yanke shawarar tashi zuwa Port Sudan,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk da ƙarancin wutar lantarki da tsadar kaya, a kullum yana tunanin buɗe rassan gidan abinci saboda akwai masu buƙatar abinci da yawa.

Port Sudan, ya zama gida ga ɗaruruwan iyalai da suka tsere wa faɗa a birnin Khartoum.

Wasu a cikinsu suna rayuwa cikin yanayi mai tsanani da cunkoso a makarantu da gine-ginen gwamnati, tare da rashin abinci da harkar kula da lafiya da kuma tsaftataccen ruwan sha.

Wata mata mai suna Batoul Tayya ta ce ita da ‘ya’yanta sun bar matsuguninsu, “godiya ga wani mai taimako da ya ba mu gidan zama”.

“Halin da muke ciki a matsuguninmu na da matuƙar wuya, don haka na yanke shawarar tafiya da yarana, na fara sayar da shayi,” in ji ta.

Labarinta, kamar na wasu mutane da yawa ya kasance abin tunawa mai ciwo da raɗaɗi na yaƙin da ya lalata rayuwar miliyoyin mutane.

Dukkanmu muna fatan za a kawo ƙarshen rikicin, nan ba da daɗewa ba domin rayuwarmu ta koma daidai.

Yanzu na dawo Alƙahira, kuma rayuwa a nan ba ɗaya ba ce da rayuwarmu ta da.

Ina kewar Omdurman da tafiyar da nake yi a bakin Kogin Nilu, da zama a ƙarƙashin bishiya da shan shayi yayin da nake hira da 'yan'uwa da abokan arziƙi da sake haɗuwa da su tare da tunawa da waɗanda muka rasa a yaƙin Sudan.