You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816577

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Bayern na tattaunawa da Tottenham kan Kane

Harry Kane Harry Kane

Bayern Munich ta shirya biyan kuɗin da ba ta taɓa kashewa a kan wani ɗan wasa don ɗaukar Harry Kane daga Tottenham Hotspur.

Shugabannin ƙungiyar za su tashi zuwa Landan domin ganawa da shugaban Tottenham Daniel Levy inda za su yi musayar ra'ayi game da ciniki ɗan wasan.

Kuɗi mafi yawa da Bayern ta taɓa kashewa wajen sayen wani ɗan wasa shi ne Yuro Miliyan 80 da suka bai wa Athletico Madrid a kan Lucas Hernandez a 2019.

Sun shirya biyan fiye da haka a kan Kane duk da yake ya rage saura wata 12 a kwantiraginsa.

A makon jiya ne, ƙungiyoyin ya kamata a ce sun gana, amma sai aka ɗage zaman, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu game da makomar kyaftin ɗin na Ingila, Kane.