You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848683

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Bayern Munich ta gwada wa Man United ƙarfi

Erik Ten Hag, kocin Manchester United Erik Ten Hag, kocin Manchester United

Bayern Munich ta doke Manchester United ci 4-3 a wasan farko a cikin rukunin farko a Champions League ranar Laraba a Allianz Arena.

Minti na 28 da fara tamaula, Leroy Sane ya ci United ƙwallo, inda Onana ya yi sakacin da ƙwallon ya faɗa raga.

Minti huɗu tsakani Serge Gnabry ya zura na biyu a raga daga baya Rasmus Hojlund ya farke, bayan da suka koma zagaye na biyu a fafatawar ta Jamus.

Tsohon dan wasan Tottenham, Harry Kane shi ne ya ci ƙwallo na uku a bugun fenariti, sai Casemiro ya zare wa United saura minti biyu lokaci ya cika.

Daf da za a tashi daga wasan ne Bayern ta ƙara ƙwallo ta hannun Mathys Tel, to sai dai Casemiro ya ƙara zare ƙwallo na biyu da ya ci a fafatawar ta hamayya.

Karon farko da aka zura wa United kwallo uku ko fiye da haka a wasa uku a jere a dukkan karawa, tun bayan da aka yi mata hakan a Disambar 1978 karkashin Dave Sexton.

Arsenal ce ta fara da cin United 3-1 a wasan Premier League ranar 3 ga watan Satumba.

Sannan Brighton ma ta zura wa United 3-1 ranar 16 ga watan Satumba a Old Trafford a dai babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wannan shi ne karo na 12 da Bayern suka fuskanci juna a gasar zakarun Turai, inda kungiyar Jamus ta yi nasara biyar da canjaras biyar ta Ingila ta ci biyu.

Tun farko an tashi 2-2 tsakanin Galatasaray da FC Kobenhavn Turkiya a daya wasan rukunin farko.

United wadda take ta 13 a kasan teburin Premier League bayan wasa biyar da fara kakar nan, tana da maki biyu.

Manchester United za ta karbi bakuncin Galatasaray a wasa na bibiyu a rukunin farko ranar 3 ga watan Oktoba a Champions League.

A kuma ranar Bayern Munich za ta ziyarci FC Copenhagen a dai daya wasan na rukunin farko.

Ranar 23 ga watan Satumba United za ta ziyarci Burnley, domin buga gasar Premier League karawar mako na shida.

Ita kuwa Bayern Munich mai rike da kofin Bundesliga za ta kece raini da FC Bochum a wasan mako na biyar.