You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816595

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Bayern Munich na zawarcin Lucas, Tottenham ta zuba ido kan Johnson

Harry Kane Harry Kane

Bayern Munich na Shirin kafa tarihin biyan fam miliyan 68 domin dauko mai tsaron gidan Faransa Lucas Harnandez mai shekara 27, idan ta saida mai kai harin Ingila Harry Kane 30, ga Tottenham. (Sky Sports)

Spurs ka iya amfani da kudin da ta saida Kane domin dauko dan wasa wasan Barcelona kuma na tsakiyar Ivory Coast Franck Kessie mai shekara 26, da kuma mai tsaron baya na Faransa Clement Lenglet mai shekara 28. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tottenham na zuba ido kan dan wasan Nottingham Forest, kuma na gaba Wales Brennan Johnson, mai shekara 22, idan ta saida Kane. (Mail)

Daya daga cikin masu kungiyar Chelsea Todd Boenhy ya bi kungiyar Barcelona a zawarcin dan wasa Paris St-Germain gaba na Faransa Kylian Mbappe mai shekara 24. (Independent)

Blues na duba yiwuwar musayar mai kai hari na Belgium Romelu Lukaku mai shekara 30, da dan wasan gaba na Serbia mai taka leda a Juventus Dusan Vlahovic mai shekara 23. (Fabrizio Romano)

Liverpool na Shirin Karin kudi domin taya dan wasan Southampton, kuma na gaban Belgium Romeo Lavia kan farashin fam miliyan 50, ya yin da kungiyoyin Chelsea da Manchester United ke zawarcin matashin dan wasan mai shekara 19. (Mail)

Liverpool na gab da kammala yarjejeniyar sayan dan wasan Leicester City, na tsakiyar Ingila Trey Nyoni mai shekara 16. (Mirror)

Da alama West Ham na gab da hakura da batun dauko dan wasan Southampton kuma na tsakiyar Ingila James Ward-Prowse, bayan kin amincewa da tayin fam miliyan 40 har sau biyu kan dan wasan mai shekara 28.(Guardian)

Burnley na tattaunawa da Arsenal, kan kwantiragi mai dogon zango kan dan wasan tsakiya na Belgium Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, ya yin da dan wasa Auston Trusty, mai shekara 24, ka iya komawa Gunners, inda Sheffield United ke sahun gaba a zawarcin mai tsaron gid ana Amirka.(Telegraph - subscription required)

Paris-St Germain ba ta shirya amincewa da tayin fam miliyan 30 da kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta sanya kan dan wasan tsakiya na Italiya mai taka leda a PSG wato Marco Verratti mai shekara 30 ba. (Fabrizio Romano)