You are here: HomeAfricaBBC2023 08 09Article 1821827

BBC Hausa of Wednesday, 9 August 2023

Source: BBC

Bayern Munich na zawarcin Kane, Al-Hilal na son Neymar

Harry Kane Harry Kane

Bayern Munich na son gabatar da tayin kusan fam miliyan 100 ga ɗan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Tottenham, Harry Kane. (Sky Sports)

Haka zalika, Bayern da Spurs na ci gaba da samun rabuwar kawuna kan kuɗin da aka sanya wa Kane, bayan sabuwar tattaunawa a kan ɗan wasan mai shekara 30 da ke son ci gaba da kasancewa a ƙungiyar ta Premier League. (Athletic - subscription required)

Ko da Kane bai bar Tottenham ba, kungiyar za ta ci gaba da kokarin dauko ɗan wasan gaba na Najeriya Gift Orban, mai shekara 21, domin samun ƙara ƙarfin bayan ƙungiyar. (Times - subscription required)

Kishiyoyin ƙungiyar ta arewacin London wato Arsenal da Tottenham, sun gama shiri domin fafatawa wajen sayo dan wasan tsakiya na Brazil, mai taka leda a Aston Villa Douglas Luiz, ɗan shekara 25. (Football Insider)

Arsenal sun kammala yarjejeniya da Brentford, domin dauko mai tsaron ragar Sifaniya David Raya, ɗan shekara 27 a kan farashin Yuro miliyan 30.(Fabrizio Romano)

Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya, na zawarcin dan wasan gaba na Brazil, mai taka leda a Paris St-Germain, wato Neymar mai shekara 32, tuni suka fara shirin ganawa da mahaifin dan wasan kan hakan. (Footmercato - in French)

Hankali kwance, Neymar zai so barin kungiyar PSG domin komawa kulup din na Saudiyya matukar za su amince ya karasa kakar wasannan a Barcelona a matsayin aro. (Sport - in Spanish)

Real Sociedad na son dauko dan wasan Arsenal, kuma na bayan Scotland Kieran Tierney mai shekara 26, a matsayin bashi a kakar wasan da muke ciki. (Telegraph - subscription required)

Kungiyoyin Leicester City da Genoa na zawarcin aro dan wasan tsakiya na Italiya, mai taka leda a Chelsea Cesare Casadei, mai shekara 20. (Sky Sport Italia - via Football Italia)