You are here: HomeAfricaBBC2023 07 29Article 1814747

BBC Hausa of Saturday, 29 July 2023

Source: BBC

Bayern Munich na son David Raya, Galatasaray za ta sayi Fred daga Man United

David Raya David Raya

Bayern Munich ta fara tattaunawa da Brentford kan golanta ɗan Spain David Raya mai shekara 27, yayin da ake cewa Yann Sommer na shirin komawa INter Milan. (Sky Sports)

Bayern ta kuma amince da tayin da Al- Nassr ta yi mata kan ɗan ƙasar Senegal Sadio Mane mai shekara 31. (Fabrizio Romano)

Wakilan Bayern sun fasa zuwa Landan domin tattaunawa da Tottenham kan ɗan wasan Ingila mai shekara 30 Harry Kane, sai dai har yanzu suna nan a kan bakarsu ta neman ɗan kwallon.(Sky Sports)

Tottenham na son amfani da damarsu ta tattaunawa da Bayern kan Kane, inda su ma za su miƙa buƙatarsu ta ɗan wasan Faransa Mathys Tel mai shekara 18.(Telegraph - subscription required)

Chelsea ta yi watsi da buƙatar Juventus ta neman aron ɗan wasan Belgium Rumelu Lukaku mai shekara 30, saboda tana son sayar da ɗan wasan baki ɗaya.(Tuttosport, in Italian)

Chelsea na son sayan 'yan wasan gaba guda uku da suka haɗa da: Michael Olise mai shekara 21 da ke Crystal Palace da ɗan wasan Lyon Rayam Cherki sai kuma ɗan wasan Ghana da Ajax mai shekara 22 Mohammed Kudus.(Football London)

PSG na dab da kammala wani cinikin abin mamaki na ɗan wasan Faransa Ousmane Dembele daga Barcelona. (ESPN)

Newcastle United ta sayar da ɗan wasan gefen Faransa Allan Saint-Maximin mai shekara 26 ga ƙungiyar Al-ahli kan kuɗi fan miliyan 30.

Manchester United ta fara tattaunawa da ɗan wasanta Dean Henderson mai shekara 26, kan shirinsa na komawa Nottingham Forest kan aro da sharaɗin saya daga ƙarshe nan da watan Janairu.(Manchester Evening News)

Galatasaray ta nuna muradinta kan ɗan wasan Manchester United ɗan Brazil Fred mai shekara 30, amma da alama akwai ba rashin daidaito tsakanin ƙungiyoyin kan farashin ɗan wasan. (Sky Sports)