You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798595

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Bayern Munich ba ta hakura da Kane ba, Al Nassr na zawarcin Onana

Harry Kane Harry Kane

Bayern Munich na shirin sake gabatar da tayi a karo na biyu kan ɗan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 29. (Sky Sport - in German)

Manchester City na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Croatia Josko Gvardiol, mai shekata 21, wanda ke tattaunawa da RB Leipzig. (ESPN)

Ɗan wasan tsakiya a Liverpool Jordan Henderson, mai shekara 33, da na Chelsea Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 34, na iya komawa kungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya bayan naɗa Steven Gerrard a matsayin sabon koci. (Mail)

Paris St-Germain na kokarin doke Chelsea, Liverpool da Manchester City a cinikin ɗan wasan Sifaniya Gabri Veiga, daga Celta Vigo. (Guardian)

Chelsea ta tattauna da Southampton kan cinikin Tino Livramento da Newcastle ke zawarci kan fam miliyan 38. (Mail)

Liverpool ta sha gaban Chelsea a farautar ɗan wasan Belgium Romeo Laviamai shekara 19 da Southampton tayi wa kuɗi fam miliyan 50. (talkSPORT)

Al-Nassr ta gabatar da tayi mai gwabi kan mai tsaron raga na Kamaru da ke taka leda a Inter Milan, Andre Onana, mai shekara 27, da Manchester United ke hari. (CBS)

Ɗan wasan Arsenal da ke buga tsakiya, Granit Xhaka, 30, zai kammala cimma yarjejeniyar £21.5m da Bayer Leverkusen a wannan makon. (Sun)

Everton ta faɗawa Almeria tana son daidaita da ita kan kwantiragin El Bilal Toure, duk da dai Fulham ta nuna tana iya shiga neman daidaita da ɗan wasan mai shekara 21 asalin kasar Mali. (Sacha Tavolieri)

Ɗan wasan Chelsea Christian Pulisic zai yi watsi da tayin da ya samu daga Lyon, a yanzu hankalinsa ya fi kwanciya da AC Milan. (ESPN)

Newcastle na gwada sa'arta kan ɗan wasan Sporting Lisbon Goncalo Inacio, mai shekara 21. (Football Insider)

Brighton na son daidaitawa da ɗan wasan Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 22, daga Ajax. (Athletic, subscription needed)

Liverpool za ta iya fuskantar kalubale daga Bayern Munich kan cinikin ɗan wasan Faransa Khephren Thuram, daga Nice. (Foot Mercato - in French)

Tottenham na kokarin cimma yarjejeniya da Clement Lenglet na Barcelona, kan kwanmtiragin shekaru uku. (Sport - in Spanish)

Tottenham na gab da daidaitawa da ɗan wasan Wolfsburg Micky van de Ven, mai shekara 22. (90min)

Wolves na shirin sayer da ɗan wasanta mai shekara 22, Max Kilman duk da cewa tayi watsi da tayin Napoli. (90min)

Chelsea na son sayar da Callum Hudson-Odoi, kuma tuni Nottingham Forest ta gabatar da tayinta kan ɗan wasan mai shekara 22. (Football Transfers)

Manchester City za ta gabatarwa Atletico Madrid tayi yuro miliyan 15 kan Rodrigo Riquelme. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Leicester City na son gwada sa'arta kan ɗan wasan Manchester City Callum Doyle, mai shekara 19. (Athletic, subscription needed)