You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218484

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: BBC

Bayanai game da rayuwar gwarazan gasar Al-Ƙur'ani ta 2021 a Najeriya

Muhammad Auwal Gusau (hagu) da Nusaiba Shuaibu Ahmad, su ne gwarazan musabaƙar Muhammad Auwal Gusau (hagu) da Nusaiba Shuaibu Ahmad, su ne gwarazan musabaƙar

Da tsakar ranar Asabar 27 ga watan Maris na 2021 ne aka kammala musabakar Al-Ƙur'ani mai girma ta Najeriya a Jihar Kano da ke arewacin kasar.

An fara musabakar ce kwana takwas da suka gabata kuma aka kammala a kwana na tara.

A ɓangaren mata, wata 'yar Kano mai suna Nusaiba Shuaibu Ahmad ce ta zo ta ɗaya.

Muhammad Auwal Gusau, shi ne gwarzon musabaƙar a bangaren maza, kuma ya fito ne daga Jihar Zamfara - ita ma a arewa maso yammacin ƙasar.

Hafizan sun gwabza da masu karatu da yawa kuma a karshe suka samu nasara a matakin karatun izu 60 da tafsiri.

An bai wa kowannensu kyautar kuɗi naira miliyan biyu da rabi bisa nasarar da suka samu.

Sannan kuma za su wakilci Najeriya a musabaƙa ta duniya baki ɗaya.

Wace ce Nusaiba Shuaibu?

"Na gode wa Allah da ya ba ni wannan nasara kuma fatana shi ne Ƙur'ani ya zama hujja a gare mu ba a kanmu ba," a cewar Nusaiba Shuaibu cikin hirarta da BBC.

Gwarzuwar musabaƙar ta 2021 ta haddace Ƙur'ani tun tana 'yar shekara 15 bayan ta fara haddar littafin mai tsarki tana 'yar 11 zuwa 12, kamar yadda ta shaida wa BBC.

Nusaiba Shuaibu Ahmad ta fara shiga gasar karatu wato musabaƙa a shekarar 2017.

Daga cikin nasarorin da ta samu, ta taɓa zama gwarzuwar musabaƙa wadda cibiyar Alfijir ke shiryawa a Kano.

Kazalika ta taba zuwa ta biyar a musabaƙar ƙasa, wadda aka gudanar a Jihar Katsina.

Suratul Jinn - sura ta 72 - ita ce ta fi bai wa makaranciyar wahala a loƙacin da take hadda. "Saboda tana da ayoyi masu kama da juna," in ji ta.

An haifi Nusaiba a shekarar 2000 a garin Kano kuma tana da miji.

Ta kammala sakandare, inda yanzu haka take zuwa jami'a.

Wane ne Muhammad Auwal?

Gwarzon musabaƙar ta maza haifaffen Jihar Zamfara ne, wanda yanzu haka yake karatun kimiyyar dabbobi (zoology) a aji na huɗu a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

Da BBC ta tambayi Muhammad Auwal Gusau cewa me ya sa bai zaɓi darasin Ƙur'ani ba a jami'a sai ya ce: "A zamanin da muke ciki, abu ne mai wuya ka ce ɓangare ɗaya za ka yi (karatu) amma yanzu zan yi karatu a jami'ar Musulunci insha Allahu."

Ɗan shekara 24, Muhammad ya fara haddar Ƙur'ani yana da shekara 10 zuwa 11.

"A lokacin da na fara (hadda) babu abin da ya fi birge mu kamar yadda ake keɓe ɗalibai 'yan ɓangaren hadda, suna gefe daban," in ji shi.

Ya ƙara da cewa surar da ta fi wahalar da shi a lokacin hadda ita ce wani ɓangare na Suratul Ɗur - sura ta 52.

"Burina yanzu shi ne Allah Ya ba mu nasara a musabaƙa ta duniya da za mu wakilci Najeriya kuma ina da ƙarin gwiwar da taimakon Allah za mu yi nasara," a cewarsa.

Hafizin ya ce yana fatan ya auri makaranciyar Ƙur'ani kamarsa a nan gaba.