You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814168

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

Barcelona za ta buga gasar zakarun turai duk da binciken UEFA

Kofin zakarun Turai Kofin zakarun Turai

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Turai (Uefa ) ta wanke Barcelona na wucin-gadi don buga gasar cin kofin zakarun Turai ta 2023-24 a wani bincike da hukumar ta Uefa ke yi kan zargin da aka yi wa kungiyar na biyan kudade ga shugaban alkalan wasa.

A watan Maris ne UEFA ta tabbatar da cewa tana duba yiwuwar biyan kudaden da Barcelona ta biya domin samun goyon bayan alkalan wasa.

Barcelona dai ta musanta aikata laifin.

Yayin da aka bai wa Barcelona izinin shiga gasar zakarun Turai, Uefa tana ikon hukunta kungiyar a nan gaba.

Binciken na Uefa ya zo ne bayan da ofishin mai shigar da kara na Barcelona ya gabatar da wani binciken laifuka a ranar 10 ga Maris.

An yi zargin cewa Barcelona ta biya Yuro miliyan 8.4 (£7.4m) ga Jose Maria Enriquez Negreira, tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalan wasa na Spain da kamfaninsa na Dasnil 95.

An tuhumi Barca da tsoffin jami'an kulob din da Negreira da laifin "almundahana", da "cin amana" da kuma gabatar da "takardar kasuwanci ta karya."

Bayanin kudaden, wanda gidan rediyon Ser Catalunya ya bayyana a watan Fabrairu, ya fito fili ne bayan wani bincike da hukumomin haraji suka yi kan kamfanin Dasnil 95, mallakan Negreira.

Barca ta amince cewa kulob din ya biya Dasnil 95, don tattara rahotannin bidiyo da suka shafi kwararrun alkalan wasa "da nufin inganta bayanan da masu horon 'yan wasa ke bukata".

Ta kara da cewa yin kwangilar rahotannin "al'ada ce a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa".