You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845881

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

Barcelona na son daukar Sancho, watakil Partey ya koma Yuventus

Jadon Sancho Jadon Sancho

Barcelona na son daukar Dan wasan gefe na Manchester United Jadon Sancho mai shekara 23, lokacin da alakarsa da Old Trafford ke kara tsami. (Sport - in Spanish)

Da yiwuwar Arsenal ta sayar da dan wasanta dan kasar Ghana, Thomas Partey mai shekara 30 kuma ana sa ran Juventus zai koma. (Football Insider)

Sheffield United na duba yiwuwar daukar tsohon koci Chris Wilder a matsayin Wanda zai maye gurbin Paul Heckgbttm Bayan kashin da suka sha a hannun Tottenham. (Mail)

Arsenal na dab da amincewa da sabuwar yarjejeniya tsakaninta da Dan wasan tsakiya na Norway Martin Odegaard mai shekara 30 inda zai rika daukar fan 200, 000 ko wanne mako. (Football Insider)

Sheffield United na duba yiwuwar daukar tsohon koci Chris Wilder a matsayin Wanda zai maye gurbin Paul Heckgbttm Bayan kashin da suka sha a hannun Tottenham. (Mail)

Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 38 zai make tsohuwar kungiyarsa Juventus kotu kan sauran kudinsa fan miliyan 17 da ba a biya shi ba a lokacin korona. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Everton na duba yiwuwar sayan Dan wasan Leeds da Italiya Wilfred Gnonto mai shekara 19, bayan gaza daukarsa da ta yi a Farkon kaka. (Football Insider)

Da yiwuwar Bayern Munich da Real Madrid su fafata a kaka mai zuwa wajen daukar tsohon Dan wasan Spain Wanda yanzu ke Leverkusen a matsayin sabon kocinsu. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tsohuwar kungiyar Luka Modric da ya fara ne neman sake daukar Dan wasan mai shekara 38 daga Real Madrid a watan Janairu mai zuwa. (90min)

Har yanzu Barcelona ba ta fara tattauna batun tswaita kwantaragin Dan wasan da Manchester United ta nema ba Dan kasar Netherlands Frankie de Jong mai shekara 26 Wanda kwantaraginsa za ta Kare a 2026. (Marca - in Spanish)