You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767611

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Barcelona gidan Messi ne a koda yaushe

Lionel Messi da shugaban Barcelona, Joan Laporta Lionel Messi da shugaban Barcelona, Joan Laporta

Shugaba, Joan Laporta ya ce Barcelona gidan Lionel Messi ne, bayan da kungiyar ke kokarin sake daukar dan wasan a karshen kakar nan.

Kwantiragin kyaftin din Argentina zai kare Paris St Germain a karshen watan Yuni, inda wasu rahotanni ke cewar zai koma Saudi Arabia da taka leda.

Sai dai a wata hira da kafar yada labarai ta Sifaniya TV3, Laporte ya ce za su kalubalancin duk kungiyar da ke son sayen dan wasan mai shekara 35.