You are here: HomeAfricaBBC2023 10 25Article 1869011

BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023

Source: BBC

Barca ba za ta yi korafi da 'yan wasanta da ke jinya a wasa da Real ba

Xavi Xavi

Barcelona ba za ta yi korafi da yawan 'yan wasanta da ke jinya idan ta zo wasan hamayya da Real Madrid a La Liga ranar Asabar ba, in ji Xavi Hernandez.

Ranar Laraba ne Barcelona za ta karbi bakuncin Shakhtar Donetsk a wasa na uku-uku a rukuni na takwas.

Barcelona tana mataki na daya a rukuni na takwas da maki shida, bayan cin wasa biyu, ba tare da an zura mata kwallo ba a raga.

Kungiyar Portugal, Porto tana mataki na biyu da maki uku, yayin da Shakhtar ta Turkiya mai maki uku ke matsayi na uku a teburi da kuma Royal Antwerp maras maki.

Barcelona mai rike da La Liga na bara tana ta uku a kan teburin La Liga, biye da Girona ta biyu, yayin da Real Madrid ke jan ragama.

Duk da yake, Barcelona na jan ragamar rukuni na takwas a Champions League, Xavi ya ce wasan da zai fuskanci Shakhtar yana da mahimmaci.

''Wannan gasar Champions League ce, babbar gasar da kungiyoyi ke gwada gogewarsu, kenan idan muka hada maki tara a wasa uku hakan yana da muhimmanci.

''Ba za mu bari hankali ya gushe a kan wasan da za mu yi ranar Asabar ba, lallai fafatawa da Shakhtar gagaruma ce, kuma ba za mu yi sake mu rasa sakamakon da muke bukata ba.''

Barcelona tana fama da rashin 'yan wasan da suka tafi jinya kamar Robert Lewandowski da Sergi Roberto da Jules Kounde da Frenkie De Jong da kuma Pedri.